Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Da Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Gana Da Shugaba Tinubu

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tare da takwarorinsa gwamnonin arewa maso yamma a ranar Alhamis sun yi ganawar sirri da shuga...


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tare da takwarorinsa gwamnonin arewa maso yamma a ranar Alhamis sun yi ganawar sirri da shugaban ƙasa Tinubu.

Ganawar sirrin tsakanin gwamnonin arewa maso yamma guda bakwai da shugaban Æ™asar ya gudana ne a fadar gwamnati na Villa dake Abuja. 

A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnonin sun ziyarci shugaban ne domin tattauna batun taɓarɓarewar tsaron da ya addabi yankin na su.

Gwamnonin sun je Villa ne domin halartar taron majalisar tattalin arziƙi na ƙasa (NEC) wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranta.

“Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, tare da takwarorinsa gwamnonin Arewa maso yamma sun yi ganawar sirri da shugaba Tinubu.

“Ganawar yana daga cikin Æ™oÆ™arin gwamnonin na neman tallafin shugaban wajen magance matsalar da ta ta’azzara na ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a a arewa maso yammaci.

“Gwamnonin sun yi wa shugaban Æ™asa bayanin babbar damuwarsu dangane da matsalolin tsaro da ba za a iya magance su ba a jihohinsu.

"Kafin ganawa da shugaban, gwamnoni bakwai (7) na Arewa maso yamma sun halarci taron majalisar tattalin arziƙin ƙasa wanda ya samu halartar gwamnonin jihohi 36."

No comments