Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mi’ara Koma Baya: Ban Taɓa Katsalanda A Aikin Mata Ta Ba - Sanata Bulkachuwa

  Tsohon Sanatan da ya wakilci Bauchi ta arewa a majalisar dattijai Najeriya, Sanata Adamu Bulkacuwa ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fasa...

 


Tsohon Sanatan da ya wakilci Bauchi ta arewa a majalisar dattijai Najeriya, Sanata Adamu Bulkacuwa ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fasara a lokacin da ya alakanta aikin matarsa da Majalisa.

Sanatan ya yi kalaman ne a zaman karshe na majalisa ta 9, inda ya yi ikirarin cewa ya yi amfani da matsayinsa wajan nema wa abokansa 'yan majalisa alfarma a wajen matarsa a lokacin da take rike da shugabancin kotun daukaka kara ta kasar.

A cewarsa tsohon shugaban majalisar dattijai ne, sanata Ahmed Lawal ya yanke masa hanzari inda ya riƙa masa katsalandan a lokacin da ya ke bayani.

"To ba a ma bar ni na karasa ba, wasu kalmomi kawai da na fara kamar cewa na gode mata, ta yi hakuri da ni, ni ina siyasa ita kuma ta na shari'a.

"Sannan taimako da na ce ta na yi, wannan dabi'arta ce, halinta ne, ba a ma jira na faɗi taimakon wadanne iri ne, dan akwai taimako iri sun fi dari, wanda kowane ma'aikaci, ko na shari'a ne ko likita ne ko injiniya ne, kowa zai iya yin taimako a kan aikinsa.

"Taimakon ba wai ya na nufin ka karya kaidar doka ko aikata abinda ba daidai ba", in ji Bulkachuwa.

Sanatan ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi masa na shiga hurumin aikin matarsa a lokacin da take aiki.

"Yadda mu ke zama da ita ban taɓa ce mata ga yadda za ki yi ba, ga yadda za ki yi shari'ar ki, ko yadda za ki yi da ofis dinki ba. Wannan maganar ma ko a gida ba ma yi".

Sai dai kalaman da ya furta sun janyo wa tsohon sanatan da matarsa, Zainab Bulkachuwa zargi .

Abin da ya faru a Majalisa

Wani bidiyon da aka naɗa da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna Sanata Bulkacuwa ya na jawabin bankwana a cikin zauren majalisar dattijai yana mai cewa:

"A cikin zauren nan, ina iya ganin fuskokin da suka zo, suka nemi taimako na lokacin da mata ta take shugabar kotun daukaka kara ta kasa".

Sai dai yana cikin bayani ne sai tsohon shugaban majaliasr dattijai Ahmed Lawal ya katse masa hanzari tare da yi ma sa hannunka mai sanda.

"Irin wadannan kalamai masu harshen damo za su iya nuna an samu alfarma ko wani abu makamancin haka", In ji shi Sanata Lawal

A yanzu haka kungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA ta aike da wasika a hukumance zuwa ga babban sufeton 'yan sandan kasar, da kuma hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC da EFCC .

Kungiyar ta nemi bangarorin uku da su gudanar da bincike a kan sanatan.

Wasu masu fafituka sun nemi a hada har da matar sa da ya ambata a cikin binciken.

-BBC Hausa

No comments