Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tabarbarewar Tarbiyyah A Arewacin Nijeriya: Ga Mafitarmu, Inji Farfesa Ango Abdullahi

  Wannan ita ce hirar da tawagar wakilan kafafen watsa labarai na garin Zariya ciki harda Editanmu Ammar Muhammad Rajab suka yi da Farfesa A...

 


Wannan ita ce hirar da tawagar wakilan kafafen watsa labarai na garin Zariya ciki harda Editanmu Ammar Muhammad Rajab suka yi da Farfesa Ango Abdullahi, tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello University Zariya, kuma shugaban kungiyar Dattawan Arewan Nijeriya. Hirar ta gudane ne a gidansa. Ga wasu bangare na hirar kamar yadda ta kasance:

SAKON TA’AZIYYAH

Da farko ya soma ne da mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar Farfesa Idris Abdulkadir, tsohon shugaban hukumar lura da jami’o’in Nijeriya. Da yake shaida halinsa ya ce mutum ne wanda ya yi rayuwa mai kyau. Ya ce a shekaru kaninsa ne na nesa. “ya yi aiki mai dadewa a ABU. Daga nan ne ganin irin kokarinsa lokacin da ake neman babban Sakataren hukumar lura da jami’o’in Nijeriya aka nada shi a mukamin. Kuma lokacin da ya jagorancin hukumar ta bunkasa kwarai da gaske. A lokacinsa ne hedikwatar ta taso daga Legas ta dawo Abuja”.

Farfesa Ango ya ci gaba da cewa; na rasa abokin aiki da muka yi aiki tare a ABU. Yana sashen ilimin dabbobi ni kuma ina bangaren noma da kiwo har na zama shugaban Jami’ar.

Za mu ci gaba da taya shi da addu’ar Allah ya jikansa da Rahama, kuma bayan da ya bari ta yi kyau. Na rasa dan uwa kuma abokin aiki. Muna addu’ar Allah ya yi masa Rahama. Allah yasa abin da ya bari a baya masu albarka ne.

Shi Marigayi ya yi aiki a ZEDA. ZEDA shi ne bunkasa ilimi. Musamman ilimi wanda muke ganin ya yi rauni ya kasa wato ilimin firamare.

YADDA AKA BAR YARA SUNA YAWO

Yanzu idan ka fita ne za ka ga yara a hanya ne a tashar mota ne. Yara da yakamata a ce suna makarantar firamare. Amma ga shi suna yawo. Iyayen gidanku ‘yan siyasa sun kasa kula da daukar al’amarin da kyau.

A bar yara ‘yan shekara shida, bakwai, takwas, tara, goma maimaikon a ce suna makaranta, suna karatu, su ginu, su wuce haka, su zama mutane wanda za su yiwa kansu amfani, su yiwa kasa amfani, sun fi so su fito su ba su sadaka. Kuma su sa su aikin banza lokacin siyasa. Su fito suna binsu suna sai ka yi, sai ka yi.

Sune kuma a daji yanzu. Sune ‘yan bindigar da ake cewa yanzu. Kuma sun soma shiga ke nan. Kuna tsammanin za su kare ‘yan bindigar? Da wadannan yaran wadanda ba su a makaranta yanzu? Idan kuna tsammanin za ku yi ta samun bacci a cikin birni, za su san inda kuke kwana.

DANGANE DA GWAMNATIN TINUBU

Da yake amsa dangane da yadda sabuwar gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu ta zo ana tsamanin a samu sauki, sai ya kada baki ya ce; “wacce? Wacce gwamnati? Kana nufin wanda Buhari zai bayar da wuri (ya bayar da wuri)? To wannan sai ku jira ku gani. Ka san karin maganar da ake cewa ‘tashi kasa koma dabe?’ Ko kuma ‘ba cinya ba kafar baya’.

DANGANE DA GWAMNATIN BUHARI DA TA SHUDE

Ina da hakki na ga abin da ba a yi daidai ba na yi magana a kai. Ko da wani zai ji haushi bai dame ni ba. Musamman wannan tafiyar da (ta kare yanzu), ai mun sha magana a kai. Ni na sha magana a kai cewa da muna tsammanin Buhari kitse ne ashe rogo ne. Hasken da muke hangowa kamar kitse, ashe rogo ne. Rogon ma ashe ganji ne. Saboda haka gwamnatin nan da ta shekara takwas (ta wuce) ta fadi warwas. A kowanne bangare ta gaza. A kowanne bangare idan ka duba kididdiga, ta fadi warwas.

A bangaren kididdigar ci gaba ka duba da kyau, a ina Nijeriya take? Amma ni na fi kishin arewa kafin na yi kishin Nijeriya. Saboda haka sai ga ‘yan Arewar kuma sun kai sun sayar. An ba su taliya da naira dubu biyar ku ka sayar. To ku shirya ku dandani kudarku. Yanzu ne za ku ji jiki magayin sosai.

MUTANEN AREWA SUN SAMU IYAYE NA KIRKI

Mu mutanen Arewa Allah ya ba mu sa’a mun yi iyaye na kirki, mun yi Malamai na kirki, mun yi shugabanni na kirki. Tushenmu mai kyau ne. Muka zo muka lalata. Ku je wajen Yayanmu ku ji irin wannan. Alhaji Aminu Dantata ya ce mutanen Arewa duk abin da ya same mu mu daina koke-koken banza mu muka ja wa kanmu. Wannan kuma haka yake. Dukkanin abin da iyayenmu suka gina; ku nuna min guda daya wanda yake tsayyaye yanzu? Ina Bankin Arewa? Arewa yanzu ba ta da wani banki babba wanda za ta ce na ‘yan arewa ne kamar yadda ake da su ashirin da bakwai din nan (mega Banks), ba ku da komai a ciki. Ina NNDC? Ina ma’aikatun Textiles? Ina Oils Mills?

A dawo wajen irin sana’arku (aikin jarida), ina New Nigerian? Duk kun kashe. Kuma sai na ce ni ina cikin wadanda suka kashe ta. Domin ina raye, ina cikin manya. Shiyasa ba mu da hujja da koke-koke irin na banza wanda ake yi. Ba ga shi yanzu aka kammala zabe ana bayar da taliya da dubu biyar ana jefa kuri’a a inda za a sha wahalar banza ba na shekara takwas.

Saboda haka laifi yana nan gida, idan za a gyara a nan gida za a gyara. Kuma yanzu ne za a yi muku ramuwar gayya. Kila ba ku san su ba ko? Mun san su.

MUN YI KARATU A KYAUTA HARDA ALAWUS

Iyayenmu sun yi mana komai. Na je makarantar Elementary kyauta. Na je Sakandare kyauta. Na je Jami’a kyauta harda alawus, da yunifom da littafai. Gida da waje harda kasashen waje kyauta. Kobo ban biya ba. Kuma lokacin babu kudin wani abu wai shi mai. Sai kudin gyada da auduga. Da shi duk suka yi wannan. Sai da na je makarantar Sakandare a Barewa. Sakandare biyu kawai ake da su a arewacin Nijeriya a lokacin; Kwalejin gwamnati na Keffi wanda aka yi a 1953, amma kafin shekara goma sha biyu su Sardauna sun kai matakin da ya ce a gina Jami’a a Samaru. Shiyasa ya mutu bai bar gida irin wannan ba (gidana da nake ciki). Ina mai tabbatar muku wannan din da kuke ciki (gidana) sai da na shekara goma sha bakwai ina biyan bashi.

Ba kudin sata bane irin wanda kuke danashe da shi. Abubuwa sun lalace a hannunmu. Saboda haka idan muna son abubuwa su gyaru da hannunmu za mu gyara shi. To alama ya nuna hannun ya kusan tsinkewa.

ILIMI YA KAMATA YA ZAME MA MAKAMIN INGANTA RAYUWARKA NE

Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da yadda tsarin karatu yake a yau da rashin aiki da ake fama da shi ganin yadda dalibai suka dogara da aikin gwamnati, kuma yanzu aikin gwamnatin babu shi, Farfesa Ango Abdullahi ya ce gazawa ce ta tsarin gwamnati. A cewarsa ilimi makami ne na ci gaban dan Adam da zamantakewarsa.

Ya ce; wanda ya samu ilimi ya samu hanyar bunkasa kashin kansa. Idan ya yi karatun da ya hango wani yana da sha’awa zai saya, shi ne maganar aiki ya taso. Zai je ya yi amfani da wannan ilimi ya yi kwadago a biya shi. Idan babu wannan daman a kwadago ko a gwamnati ko a kamfanuka masu zaman kansu, wannan ilimin yakamata ya zama ya samar ma abin da za ka iya rayuwa da shi. Saboda haka ba daidai bane a ce idan na je makaranta sai na samu aiki. Ko iyaye su ki kai ‘ya’yansu makaranta domin wadanda suka kai da farko sun yi karatun ba su samu aiki ba. Me ke nan? Wannan na daga cikin matsalolin.

Gazawar tsarin gwamnati da aka kasa ilmantar da mutane su fahimci mene ne ma’ana da kuma dalilin da ya sa a daidaiku kake da bukatar ilimi. Ka guje ma jahilci domin jahilci ba inda zai kai ka sai rashin nasara.

RASHIN TARBIYYAR ‘YA’YANMU A YAU YANA DA ALAKA DA GAZAWAR IYAYE, AL’UMMA DA SHUGABANCI

Dangane da rashin tarbiyyah da ake fama da shi a yau kuwa, Farfesa Ango Abdullahi ya alakanta hakan da gazawar iyaye, al’umma da shugabanci. Inda ya ce; akwai gazawar al’umma da kuma shugabanci. Alal misali; a halin da ake ciki yanzu na talauci a Arewa wanda zai sa matanmu da ‘ya’yanmu da iyaye za su fito suna rububin kwalin taliya da naira dari biyar a ce ga inda za ta jefa kuri’a; ka san wannan gida (babu tarbiyya).

Jiya a nan ina hira da wani Hakimi nake ce mishi mu shiga cikin birnin Zazzau, idan an kirga gida goma, da kyar za ka kirga gida biyu suna abincin safe suna yin abincin rana harda na da daddare. Abinci sau uku ke nan. Amma mafi yawan sauran ko sau daya ne ko ma babu. Kuma ga ‘ya’ya suna ta haihuwa. Matan da suke gidan ba a lura da su ba, suma shiyasa suke fitowa cikin wannan hali suna rububin taliya ba tare da tunanin ma abin da ya fito da su zabe bane. Ko me yasa ake zabe. Duk wannan ba ya cikin tunaninsu. Me yasa ake zabe? Fitar da shugabanni wadanda za su zo su gina abin kirki shi ne dalilin bayar da damar zabe. Wanda suka kasa, wannan zabe ya zo a ture su a kawo wadanda za su iya. Amma idan an zo da naira, ita ake wawa, ba maganar ci gaba ba.

Saboda haka nan, ka ga wanda ya kasa lura da iyali a gida, ga ‘ya’ya ya haifa da yawa. ‘Ya’yan ma kila ba su samun wurin kwana a gidan. Sai sun je makwabta ko wajen abokansu su kwana. Ka ga idan sun kwana a gidan ma ba su san ina kwana tsakaninsu da iyayensu ba. Sannan idan suna tunanin wannan iyayensu ne sai su ce; to wannan iyayen namu mene ne hakkinsu a kanmu? Suna cin abinci a wani gida ne? Ka ga idan sun ki gaida iyayen ba mamaki. Balle a ce sun zauna a gida suna neman a koya musu tarbiyyar gida da sana’ar gida da sauran su, babu! Shiyasa abin yake zama karazube. Kuma lamarin na sake tabarbarewa.

BATU AKAN ALMAJIRCI

Maganar almajircin nan da sauran su duk shakiyanci ne ni a wurina na iyaye. Shakiyanci ne. Ka haifi dan sannan yana da shekara shida ko bakwai sannan ka tura wani ya lura da shi; kai da ka haife shi fa? Ah ai ya je gabas ne ya je karatu, karya kake yi! Ka kasa lura da shi ka kore shi a gidan.

Ni yanzu idan ina da mulki; da farko ba Malamin da zan bar shi a nan Zariya sai ya kawo rajista na ‘ya’yan da suke tare da shi. A ina ka dauko? Wa ya baka su? Da ya baka su ka dauko kai za ka ba su abinci? A’a, ai ranka ya dade bara za su yi; bara a gidan wa za su yi bara? Saboda me?

Kuma idan ya tashi da safe, kalace yake nema ba ya tunanin karatu. Kafin a ce haka rana ta yi yana tunanin abincin rana, kafin ranar ta karya yana tunanin zai je ya kwanta da yunwa. Saboda haka yana bara duk ranar tunda ya tashi. Yaushe aka yi karatun? Idan banda karya.

Sai na kuma uban yaron a kai shi kurkuku, kuma hukuma ta lura da dan. Ko ba shi ke nan ba? Saboda haka nan akwai aiki gare ku, ko ku yi da lalama, ko ku yi da akasin lalama. Amma wadanda ake fama da su yanzu ai kwanan nan suka zo.

MUN BA DA SHAWARAR YADDA ZA A TSAIDA BOKO HARAM

Mu muka yi kokari mu kashe Boko Haram, ni na rubuta kundin bayanan da aka bai wa Jonathan ya yi kokarin yadda za a tsaida Boko Haram da wuri, ba su bi ba. Suka ce; a’a rabau da su wannan ‘yan almajirai ne masu tsumma. To ga shi sun gagari gwamnatin ko? To haka wannan da ake fama wadannan ‘yan yaran. ‘Ya’yanmu ne da jikokinmu, ko ruwansu aka yi? Ba zubowa suka yi daga sama ba, ‘ya’yanmu ne. Jiya wani yake ba ni labari wasu sun zauna suna hira, sai ya ce shi da ya san inda ‘yan ‘bandit’ din suke tunda ana samun abinci a wurinsu, da ya je ya shiga.

JAN KUNNE GA ‘YAN JARIDA

To wannan abu yana hannunku (‘yan jarida)`, ku je ku yi ta yi ma iyayen gidanku kirari; sai sun yi, sai sun yi, ko da aikin banza za su yi. Ku iske abin da muke ciki yanzu. Don abin zai kara lalacewa.


GA MAFITARMU

Idan ka yi barna wa zai gyara maka? Kai za ka gyara? Ko zan tashi ne na yi wauta a nan, ga dakin yara can, a je a yi bayan gida a kofar dakin, na koma daki da wadansu Malamai masu dogon gemu a ce a taya ni addu’a? Ina so kafin gari ya waye na ga ba bayan gidan nan. Ni na yi fa. Addu’a ta kwashe min bayan gida, idan gari ya waye zan zo na iske shi, in dai ba ina da mayunwacin kare bane ya zo cinye.

Saboda haka barnar da ka yi kai za ka gyara. Ba za mu jira kowa ya zo ya yi ma. Wannan kuma shi ne bangaren matsalar tunaninmu da fikirarmu a nan Arewa. Cewa muna jiran wani mu’ujiza (magic). Allahn da ya halicce mu ya ba mu kundin shari’arsa. Idan kai ma kirista ne ya ba ka kundin shari’arsa. Ana bin shari’ar Allah din ne? Da ana bin Kur’anin da kyau ai da ba ma cikin wannan (halin da muka fada a ciki). Da ana bin baibul din ma da kyau ma da ba a cikin wannan. Duk ba su ake bi ba ai. Saboda haka shi ke nan kuma sai ka yi wauta sai ka koma wajen Allah da yake ka raina kofar gidanshi ka je kana surutun banza. Idan ka yi barna, kai ne mai gyarawa.

 

No comments