Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabon Kwamandan NSCSC Ya Ɗau Alwashin Magance Manyan laifuffuka A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim A yanzu haka da 'yan Bindiga suka ci gaba da karshe-karshe mutane da garkuwa da su, Sabon Kwamandan ru...


Daga Hussaini Ibrahim

A yanzu haka da 'yan Bindiga suka ci gaba da karshe-karshe mutane da garkuwa da su, Sabon Kwamandan rundunar farin kaya watau NSCSC, Sani Mustafa ya dau alwashin magance matsalar tsaro da manyan laifufuka da suka addabi jihar Zamfara.

Kwamnadan Sani Mustafa ya bayyyana haka ne a lokacin da ya ke amsar kujerar shugabancin a hannun takwaransa me barin gado Muhammad Bello Ma'azu a Hedikwatar da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara. 

A nasa jawabin, Kwamanda Sani Mustafa ya yi alkawarin bayar da duk gudunmawarsa wajen yaki da matsalar tsaro da masu aikata laifuka a jihar. 

Don haka Kwamandan Sani Mustafa ya umarci dukkan jami’an rundunar da ke jihar Zamfara da su guji cin mutuncin jama’a, su guji cin zarafin jama’a amma su kasance masu tsayin daka da da’a wajen gudanar da ayyukansu.

Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne gabatar da tutar hidimar rundunar da Kwamanda Muhammad Bello Mu'azu a mai barin gado zuwa ga kwamandan mai jiran gado, Kwamanda Sani Mustafa.

Kwamnadan mai barin gado ya bayyana nasarorin da ya samu zuwansa jihar ta Zamfara, ta kokarinsa na magance matsalar tsaro da manyan laifuffuka da kuma ci gaba jami'an rundunar na karin girma ga ma'aikatan da dai sauran su.

A halin yanzu, Kwamanda Muhammad Bello Mu'azu ya fice daga rundunar NSCDC ta jihar Zamfara zuwa inda aka yi ma sa canjin wurin aikin.

No comments