Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Sanda Sun Ƙwato Motocin Da Matawalle Ya Kwashe Bisa Umurnin Kotu, Inji Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara, ta yi ƙarin haske dangane da samamen da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta jagoranta wanda ya kai ga ƙwat...


Gwamnatin jihar Zamfara, ta yi ƙarin haske dangane da samamen da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta jagoranta wanda ya kai ga ƙwato motocin da tsohon gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle ya kwashe.

Da sanyin safiyar ranar Juma’a ne, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kai farmaki gidan tsohon gwamnan, inda aka kama motoci sama da guda 40.

A wata sanarwa da aka fitar a yau a Gusau, Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya shaida cewa ‘yan sanda sun ɗauki matakin kai farmakin ne bisa umurnin kotu kuma sun samu sammacin gudanar da bincike a gidan.

Sanarwar ta ƙara da cewa; “Idan za ku iya tunawa gwamnatin jihar Zamfara ta aika ma tsohon gwamna Bello Matawalle da mataimakinsa a hukumance kan su dawo da dukkanin motocin da suka ɓata cikin kwanaki 5 na aiki”.

“Mun kuma shigar da ƙara a hukumance zuwa ga hukumar ‘yan sanda akan yadda aka take buƙatar al’umma aka ɓarnatar da dukiya ta hanyar sace kayayyaki masu daraja da ya haɗa da motocin gwamnati.

“A bisa haka ne, ‘yan sanda suka nemi sammacin bincike wanda kotu ta ba su, wanda hakan ya sanya suka kai farmaki gidan Matawalle da ke Gusau, ƙaramar hukumar Maradun, da kuma wata maɓoyar da ba a bayyana ba.

“Sama da motoci 40 ne aka ƙwato wanda suka haɗa da motoci masu tare harsashi guda uku da kuma ƙirar SUV guda takwas.

“Muna son mu sake jaddada aniyarmu na ƙwato dukkanin wani abu mallakin al’umma. Manufarmu ɗaya ita ce ceto da sake gina Zamfara. Ƙwato kayayyakin da aka sace tare da kuma ƙadarorin al’umma yana daga muhimmin ɓangare na aikin cetonmu.

“Muna so mu yi kira ga al'ummar Zamfara da su kwantar da hankalinsu a yayin da muke ci gaba da samun gagarumin ci gaba a fannin tsaro da kuma matsalar ƙarancin ruwa a jihar.”

No comments