Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Taron Dangi Ne Aka Yi Mun Na Faɗi Zaɓe A Majalisa, In Ji Abdulaziz Yari

  Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata a Majalisar dattijai ta Najeriya, ya yi ikirarin cewa taron dangi aka yi masa, aka kayar da shi a...

 

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata a Majalisar dattijai ta Najeriya, ya yi ikirarin cewa taron dangi aka yi masa, aka kayar da shi a takarar da yan yi ta neman shugabancin majalisar dattijai ta 10.

Sanata Abdulaziz Yari ya shaida wa BBC cewa zaɓen ya zo masa da mamaki saboda har zuwa lokacin da aka kai ga zaɓen yana da kwarin guiwar samun nasara.

Sai dai duk da haka sanatan ya ce ya amince da shan kaye.

"Zaben majalisa, ba zaɓe bane da ake yi wa jayayya a ce ko an yi maguɗi, babu magudi a cikinsa, mu 109 ne kuma kowa zai zo da ra'ayinsa, da abinda hankalinsa ya ba sa ya yi, kuma sun yanke hukunci".

Sanatan ya kuma ce da ya san ba zai ci zaɓen ba tun farko da bai tsaya takarar neman shugabancin majalisar dattijan ba.

Ya yi ikirarin cewa a ranar da su fara daukar sakamako na mutanen da ke mara masa baya sun samu adadi da zai sa su iya samu rinyaje a zaɓen.

Sai dai ya yi zargin cewa taron dangin da aka yi masa ya sa ya sha kaye.

"Shugaban kasa na ciki, mataimakin shugaban kasa na ciki, haka sakataren gwamnati na ciki da gwamanoni, ni kadai ne sai waɗannan bayin Allah."

"Ina fatan gobe idan shugaban kasa ya dawo a karo na biyu, zai yarda dimukuruɗiyya ta dauki matakinta a cikin majalisa, ya ce yana son wane amma abin adalci ga shugaba shi ne da wannan da wannan duka na kane," in ji shi.


Sai dai duk da korafe -korafen da sanatan ya yi, ya ce dangantakar da ke tsakaninsa da shugaba Bola Tinubu ba ta sauya ba saboda ya rungumi kaddara.

"Na dauka Allah ne ya yi, ban dauka Tinubu ne ya yi ba, Allah ne ya yi, domin Allah ne ya kaddara cewa zai zamo,"in ji Yari.

Karin haske

Godswill Akpabio ya ci zaɓen ne da ƙuri'a 63 a kan abokin takararsa Sanata Abdul'aziz Yari wanda ya samu ƙuri'a 46.

Daidai lokacin da 'yan majalisar wakilai 353 suka kaɗa ƙuri'unsu ga Tajuddeen Abbas, wanda ya zama shugaban majalisar wakilai.

Sabbin shugabannin majalisar ta goma su ne suka samu goyon bayan jam'iyya mai mulki ta Najeriya wato APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Zaɓen ya kawo ƙarshen kai ruwa da rana da taƙaddamar da aka shafe watanni ana yi tun lokacin da jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu suka nuna goyon baya ga takarar Sanata Akpabio da Onarabul Tajuddeen.

Sun dai kafa hujja ne da cewa tun da Bola Ahmed Tinubu, shugaban ƙasar da mataimakinsa Kashim Shettima, duka Musulmai ne, ya fi dacewa a samu Kirista daga Kudancin Najeriya ya zama shugaban majalisar dattijai.

Shi ne mutum na uku mafi girman muƙami bisa tanadin doka a Najeriya.

A cewarsu matakin zai tabbatar da daidaito wajen raba muƙamai da inganta haɗin kan ƙasar mai al'ummomi da addinai mabambanta.

Sai dai masu sukar matakin sun ce abin da APC da Shugaba Tinubu suka yi tamkar katsalandan ne cikin harkokin Majalisar Tarayya wadda tsarin mulki ya ba ta 'yancin cin gashin kanta.

No comments