Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Neman Afuwar Musulmai Kan Kalamaina – Kashim Shettima

Maitamakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya ce yana neman afuwar al'ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaɓen s...


Maitamakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya ce yana neman afuwar al'ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaɓen shugabannin majalisar dokokin Najeriya.

A cewarsa ba a fahimci maganar a muhallinta ba, kuma ba shi da wata manufa na ɓata sunan addininsa.

Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi waɗannnan kalamai ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama'a yana bayani a kansu ba.

Sannan yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar ƙasar baki-ɗaya.

Kalaman Shettima a cikin makon jiya sun haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta inda aka riƙa sukar mataimakin shugaban ƙasar.

Sai dai Kashim Shettima ya ce shi Musulmi ne na haƙiƙa domin zuri'arsu sun shafe tsawon dubban shekaru a kan tafarkin addinin.

Sannan duk wanda bai jidadin kalamansa ba, ya yi hakuri a yafe masa, ba shi da niyyar cutar da addini.

"Ni ɗan adam ne kuma ajizi don haka ina neman afuwar al'umma da Ubagijina".

Kashim Shettima ya tunasar da cewa shi ɗan malamai ne kuma jikan malamai, don haka ba shi da niyyar muzantawa wani ɓangare na addinin kasar.


No comments