Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Muka Dakile Yunkurin El-Rufai Na Rushe Kotunan Shari’ar Musulunci A Kaduna, Inji Kakakin Majalisar Jihar

  Daga Zailani Mustapha Tsohon Kakakin majalisar jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Ibrahim Zailani ya yi bayanin yadda suka dakile tsohon gwamna...

 


Daga Zailani Mustapha

Tsohon Kakakin majalisar jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Ibrahim Zailani ya yi bayanin yadda suka dakile tsohon gwamnan jihar Kaduna daga rushe kotunan shari’ar Musulunci da kuma kotunan shari’ar gargajiya a fadin jihar. kamar yadda jaridar MADOGARA ta labarto.

Zailani ya bayyana hakan ne a jawabin bankwana da ya yi kan kammala wa’adin mulkinsa a matsayin Kakakin majalisar a ranar Alhamis 8 ga watan Yunin 2023. Inda ya ce ba don jajircewarsa ba da yanzu tsohon gwamnan ya gadar da fitinar da Allah kadai ya san inda za ta tsaya.

Zailani ya soma bayaninsa ne da godiya ga Allah bisa kammala wa’adin mulkinsa a matsayin Kakakin majalisar lafiya, inda ya ce; “Yau rana ita ce ta karshe a wannan a majalisa ta Tara. Ya zama dole mugode ma mutanen jihar Kaduna da ‘yan’uwana ‘yan majalisa da suka ba mu dama muka zauna a wannan kujera na tsawon shekaru uku da ‘yan watanni a matsayina na Kakakin majalisar jihar Kaduna. Ya zama dole bayan mungode ma ‘yan majalisa, mugode ma ma’aikatan majalisar jihar Kaduna. Duk nasarar da aka samu wallahi da ba su ba za a samu ba. Da kunci da aka shiga iri daban-daban amma suka tsaya tsayin daka domin tabbatar da an yi abin da yakamata”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “mun ga abubuwa iri daban-daban mun kuma gode ma Allah, da ya kawo mu irin wannan rana mai albarka. Sai dai mulki Allah ke da shi, kayanshi ne, ya kan ba wanda ya so a lokacin da ya so”.

Zailani ya ce ya gamu da tarnaki iri daban-daban, kuma abubuwa marasa dadi da mai dadi sun faru. “Kuma ya zama dole ba zan kulle gidan nan ba, sai na yi bayani a kan su. Ina na fito, ina nake, ina kuma nake fatan mu tafi. Abin da ya fi tayar min da hankali, na roki duk wanda ya yi min ba daidai ba a jihar Kaduna na sani ko ban sani ba don Allah ya yafe min. Wanda kuma ya yi min da gangar ko kuma bisa kuskure, wallahi na yafe mishi”, ya tabbatar.

Sai dai ya ce ko a yau ya bar majalisar jihar Kaduna to ya gode ma Allah, inda ya yi bayanin dalilan da yasa ya fada masifu daban-daban a yayin rike da jagoracin Kakakin majalisar jihar. “Dalili guda daya abin da ya sa na shiga masifu daban-daban; akwai doka wanda aka so da shi wannan gidan (majalisar), na ci wuya iri daban-daban da ya ba ni iko na tsaya da goyon bayan ‘yan’uwana ‘yan majalisa dokarnan ba ta tabbata ba”.

Ya kara da cewa; “Ba wata doka bane illa doka da aka turo min 30 ga watan Janairu shekara ta 2023 wanda aka turo dokarnan cewa ana son a share kotunan shari’ar Musulunci a jihar Kaduna, a kori kotunan shari’ar gargajiya a jihar Kaduna wanda bai tabbata ba. Saboda haka ni ko a nan na tsaya, wallahi tallahi na godema Allah”, ya lurantar.

“duk masifar da na shiga wannan doka ita ta ja min. Kuma ba ni da na sani ko na minti na daya. Ni ina da Sarauta na Garkuwar Alkur’ani mai girma a ce na zo na share kotunan shari’ar Musulunci da kotunan shari’ar gargajiya wanda mutane da yawa sun hallaka wajen tabbatar da wadannan kotuna guda biyu a ce mu koma Area Court na da can, wallahi na godema mutanen da suka ba ni dama na zama dan majalisa. Ko da shi kadai ne aikin da na yi a matsayin dan majalisa” ya ce. 

Zailani ya ce tabbas kudurin wannan doka ma kokarin tada fitina ne a jihar Kaduna; “Domin wannan abin da ta fita wallahi da fitinar da zai biyo baya a jihar Kaduna Allah kadai ya sani. Saboda haka wannan doka ina rokon ‘yan’uwana ‘yan majalisa da wani ya shigar da kuduri na watsi da wannan dokar da aka turo domin ya zama a tarihin wannan doka an yi watsi da ita”, ya roka.

Bayan wannan rokon da Zailani ya yi ne, nan take aka yi watsi da dokar, wanda wannan ya zama shi ne aiki na karshe da Yusuf Ibrahim Zailani ya yi a matsayinsa na Kakakin majalisar jihar Kaduna.

“wannan doka da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya kawo, an mayar da wannan doka, ba a amince da ita ba. An yi tir da ita”, ya jaddda.

 

No comments