Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Tsoffin Daliban Jinya Na Jami'ar MAAUN Sun Wayar Da Kan Ɗalibai Mata Kan Cututtuka Masu Yaɗuwa

Daga Muhammad Farouk Kungiyar tsofaffin daliban Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN) ta wayar da kan d...


Daga Muhammad Farouk

Kungiyar tsofaffin daliban Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN) ta wayar da kan dalibai mata hanyoyin da za su kare kansu daga cututtuka a Kano. 

Daliban Jami'ar wadanda suka karanci aikin jinya sun kai wata ziyara ta wayar da kan daliban makarantar Sakandare ta mata ta 'Kano Capital Girls Secondary School'. 

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani Kakakin kungiyar Sadiq Abubakar Ado ya ce sun shirya taron wayar da kan matan ne domin sanar da su hanyoyin da za su kare kansu daga cututtuka musamman masu yaduwa.

"Da yake mata suna jinin al’ada to akwai bukatar matan su san yadda za su kula da kansu saboda lokaci ne da za su iya daukar cututtuka saboda yanayin halittarsu”, inji Sadiq Ado.

Ya kuma ci gaba da cewa mata da yawa su kan dauki cututtuka a bandaki wato 'UTI infection' wanda hakan ya kan haifar musu da matsalolin, wanda ya ce hakan ce tasa suka je makarantar domin wayar da kan su domin su gujewa duk abubuwan da ka iya haifar musu da matsala.

”Wannan aiki da muka koyo na tallafawa al’umma mai makarantarmu ta MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne muke koyi da shi wajen tallafawa na kasa da gajiyayyu da dalibai baki daya. Ganin haka ne shiyasa muka ga dacewar mu yi koyi da shi daidai karfinmu tunda ba za mu iya yin yadda yake yi ba domin mu nuna cewa daga wannan makaranta muka koya wannan dabi'u masu kyau”, inji Kakakin kungiyar. 

Sadiq Abubakar Ado ya kara da cewa a lokacin watan Ramadana sun kai tallafi gidan marayu, suka tallafa musu da kayan sawa da na masaruti, shiyasa a wannan karon suka zabi su kai wannan tallafi wannan makarantar, kuma sun raba audugar mata ga mata 50.  Ya ce ba audugar kadai suka ba su ba, sun hada musu ma da wasu kayayyaki na ci da sha. 

Wakiliyar shugabar makarantar ta Kano Capital, Hajiya Maimuna Nuhu ta ce sun yi farin ciki da zuwan wannan kungiya wanda suka je suka wayar da kan daliban da kuma kayan da suka raba musu. 


A zantawarmu da daliban su ma sun nuna farin cikinsu bisa wannan tallafi da aka ba su. Inda suka nuna matukar gamsuwarsu bisa ga wannan tallafi.

No comments