Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Fara Aikin Hanya A Gusau

  Gwamna Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya Ƙaddamar da fara aikin yin sabbin hanyoyi a birnin Gusau, duk a cikin shirinsa na sabunta biranai. ...

 

Gwamna Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya Ƙaddamar da fara aikin yin sabbin hanyoyi a birnin Gusau, duk a cikin shirinsa na sabunta biranai. 

Sashen farko na wannan aikin za a fara ne da yin hanyoyi guda haɗu masu tsawon kilomita 3.1, wanda kuma za su haɗa da manyan kwalbati da sauransu. 

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce an yi bikin ƙaddamarwa ne a titin Gidan Sambo, daura da ofishin 'yan sanda dake Gusau. 

Ya ƙara da cewa, wannan aiki na hanyoyi yana daga cikin alkawurran da Gwamna Dauda ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe; cewa zai sabunta biranai, ta hanyar gina ingantattun hanyoyi. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa: "A wurin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta sabunta biranai a faɗin Jihar Zamfara, lamarin da aka rasa a gwamnatocin baya. 

"Sashen farko na aikin zai zagaya shatale-talen Bello Barau zuwa Hanyar Babban Ofishin 'Yan Sanda, zuwa gidan Gwamnati, zuwa Kwanar 'Yan Keke, zuwa fadar Sarki, zuwa Tankin Ruwa. 

"Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi imanin cewa idan aka samar da hanyoyi masu inganci tare da bunƙasa biranai zai kawo wa Jihar masu zuba hannun jari. 

"Haka nan kuma Gwamna Dauda ya nemi alfarmar jama'ar Gusau da su yi haƙuri da duk wata takura da aikin zai haifar, saboda za a mori alfanunshi masu yawa."

No comments