Daga Zailani Mustapha A kokarin da Jaridar MADOGARA ke yi wajen bunkasa ayyukanta bisa doron zamani da ka’idar aikin Jarida, jaridar ta sa...
Daga Zailani Mustapha
A kokarin da Jaridar
MADOGARA ke yi wajen bunkasa ayyukanta bisa doron zamani da ka’idar aikin
Jarida, jaridar ta sauya tambarinta domin ya dace da manufofinta da
kudurorinta.
Wannan bayanin ya fito
ne daga bakin Babban Editan Jaridar, Ammar Muhammad Rajab a wata sanarwa da ya
sanyawa hannu a ranar Alhamis din 17 ga watan Agustan 2023.
“mun sauya tambarin ne
domin jaridar ta bambanta da sauran shafuka tare da inganta ayyukanmu”, in ji
sanarwar.
Sannan har wala yau
sanarwar ta ce ta sauya shafin Intanet dinta daga ( www.madogara.com.ng ) zuwa www.jaridarmadogara.com.ng domin
gudanar da ayyukan jaridar cikin inganci.
Sanarwar ta kara da
cewa; jaridar mallakin kamfanin MASSNOOR MEDIA SERVICES ne. Kuma shafin jaridar
na turanci shi ne DAILY STRUGGLE da ake buga a shafin intanet na www.dailystruggle.com.ng wanda ta ce
shima a nan gaba za ta zo da sauye-sauye domin bunkasa jaridar.
No comments