Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara ta nemi ƙarin dakarun sojoji saboda 'yan fashin daji

Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi ƙarin dakarun sojoji saboda kawo karshen 'yan fashin daji da suka addabi jihar. Gwamna Dauda...


Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi ƙarin dakarun sojoji saboda kawo karshen 'yan fashin daji da suka addabi jihar.

Gwamna Dauda Lawal shi ya bayyana haka a Gusau, a ranar Litinin lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, da wasu manyan jami'an runduna ta takwas a gidan gwamnatin jihar.

Gwamna Dauda ya ce yana neman ƙarin sojoji a jihar ne domin ganin an magance matsalar tsaro da jihar ke fama da shi.

Ya ce sun tattauna kan hanyoyi da za su bunƙasa aikin haɗin gwiwa don kakkaɓe ƴan bindiga da ke addabar jihar da kuma ke kawo tsaiko wajen samun ci gaba.

Gwamnan ya ce ya ji daɗin martanin da ya samu daga shugaban rundunar sojin kan irin shiri da suke yi na daƙile ayyukan ƴan bindiga da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

No comments