Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a yau Litinin, ya kai ziyarar jaje ga al'ummar ƙaramar hukumar Bungudu. A daren jiya ne dai '...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a yau Litinin, ya kai ziyarar jaje ga al'ummar ƙaramar hukumar Bungudu.
A daren jiya ne dai 'yan bindiga suka kai hari garin na Bungudu, inda suka kashe mutum É—aya tare da sace mutane shida.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnan ya kai wannan ziyara ne domin jajantawa masarauta da al'ummar garin Bungudu.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal a yayin ziyarar da ya kai fadar Sarkin Bungudu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bin hanyoyin kawo ƙarshen ta'asar 'yan bindiga.
Ya ce: "Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru domin ya jajanta mishi da ma sauran al'umma bisa harin 'yan bindiga.
"A yayin da gwamnan yake jawabi a fadar, ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi don ganin wannan matsala ta zama tarihi.
"Daga Æ™arshe ya miÆ™a ta'aziyya ga al’ummar Æ™aramar hukumar, tare da rokon su ci gaba da yin addu'o'i."
Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya yi godiya ga gwmanan bisa wannan ziyara ta jajantawa.
Ya ce, tun bayan afkuwar lamarin yake ta yin waya da Gwamna, inda ya tabbatar mishi da cewa ya ba jami'an tsaro umurni da su gaggauta ceto waÉ—anda aka sace.
No comments