Akalla sojojin Najeriya 26 ne suka mutu, kana 8 suka samu raunuka bayan da ‘yan bindiga suka yi musu kwantan bauna a jihar Neja da ke yan...
Akalla sojojin Najeriya 26 ne suka mutu, kana 8 suka samu raunuka bayan da ‘yan bindiga suka yi musu kwantan bauna a jihar Neja da ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda majiyoyin soji har biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa.
Bugu da kari, wani kakakin sojin saman Najeriya ya ce wani jirgi mai saukar ungulu da ya kai dauki ga wadanda suka samu rauni ya rikito a ranar Litinin a yankin da dakarun Najeriya ke yaki da ‘yan bindiga, sai dai bai yi bayani ko wadanda ke cikin jirgin sun tsira da rayukansu ba.
Hafsoshin sojin biyu da suka nemi a sakaya sunayensu sakamakon rashin izinin ganawa da manema labarai, sun ce sojoji 23 ne suka mutu tare da mayakan sa-kai 3, sakamakon mummunan bata-kashi da aka yi a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina.
Wata majiya kuma ta ce ‘yan bindigan sun yi asarar dimbin mayakansu. Ta kuma ce jirgi mai saukar ungulun da ya fadi yana dauke da gwawarwakin dakaru 11 da suka mutu tare da 7 da suka samu raunuka, tana mai cewa jirgin ya fadi ne sakamakon wuta da ‘yan bindiga suka bude masa.
A wata sanarwa, wani kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gwabket ya tabbatar da faduwar jirgin, inda ya ce ya kwashi dakarun da lamarin ya rutsa da su ne daga makarantar firamare ta Zungeru, amma ya rikito a kauyen Chukuba na karamar hukumar Shiroro a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
Yankunan arewa maso yammaci, da tsakiyar Najeriya sun shafe tsawon shekaru suna fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke kisa da kuma sace mutane don karbar kudin fansa, tare da kona gidaje da kuma satar kadarori.
No comments