Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Harry Kane ya koma ƙungiyar Bayern Munich kan yarjejeniyar shekara huɗu. Tafiyar tasa ta kawo ƙ...
Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Harry Kane ya koma ƙungiyar Bayern Munich kan yarjejeniyar shekara huɗu.
Tafiyar tasa ta kawo ƙarshen taka leda na shekara kusan 20 da ya yi a Tottenham.
Bayern ta ɗauki ɗan wasan gaban kan yuro miliyan 100 haɗi da tsarabe-tsarabe, kuma akwai yiwuwar zai buga wasan ƙarshe da za ta buga da RB Leipzig a gasar German Super Cup a yau Asabar.
Kane mai shekara 30 ya bar Tottenham a matsayin ɗan wasan da ya fi ci mata ƙwallaye - 280 cikin wasa 435.
Cikin wani saƙo a shafukansa na zumunta, Kane ya ce "na ji a raina cewa lokacin barin Spurs ya yi".
No comments