Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ministocin da aka rantsar a yau an zaɓo su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da la...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ministocin da aka rantsar a yau an zaɓo su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
"Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku." - In ji Tinubu
Ya ƙara da cewa "Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati."
Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.
Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”
A watan Afrilu ne shugaban na Najeriya ya miƙa wa Majalisar Dattijan ƙasar sunayen mutum 45 domin tantantancewa a matsayin minsitoci.
Bayan haka nan shugaban na Najeriya ya bayyana ma'aikatun da kowane minista zai riƙe gabanin ranar ta yau da ake rantsarwar.
Sai dai ko a ranar Lahadi, shugaban ya fitar da wasu sauye-sauyen da ya yi na ma'aikatu ga wasu sabbin ministocin.
Jerin ministocin Tinubu

Ma’aikatar kuɗi da tattalin arziƙi - Wale Edu
Ma’aikatar sadarwa da ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arziƙin dijital - Bosun Tuani
Ma’aikatar harkokin tattalin arziƙin teku - Bunmi Tunji-Ojo
Ma’aikatar sufuri - Adegboyega Oyetola
Ma’aikatar wutar lantarki - Adebayo Adelabu
Ma’aikatar ma’adanai - Dele Alake
Ma'aikatar shari'a Lateef FagbemiMa’aiktar yada labarai da wayar da kan jama’a – Muhammad Idris
Ministan Ilimi -Yusuf T. Sununu
Karamin ministan gidaje da raya birane -Abdullahi T Gwarzo
Ministan ayyukan gona da samar da abinci -Abubakar Kyari
Ministan Ilimi – Tahir Mamman
Ministan harkokin cikin gida -Sa’idu Alkali
Ministan harkokin waje – Yusuf Tuggar
Ministan lafiya – Farfesa Ali Pate
Ministar al’adu – Barista Hannatu Musawa
Ministan wasanni - John Enoh
Ministan sufurin jirgin sama - Festus Keyamo
Karamar ministar Abuja – Mairiga Mahmud
Ministan Ilimi da fasaha - Uche Nnaji
Ministar harkokin mata – Uju Kennedy
Ministan ayyuka - David Umahi
Ministan ma'aikatar Neja-Delta - Abubakar Momoh
Tinubu ya yi wa ministoci sauyin ma'aikatu
Gabanin rantsar da sabbin ministocin, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sauyin ma'aikatu ga wasu ministocinsa a ranar Lahadi.
Inda aka mayar da Adegboyega Oyetola zuwa ma’aikatar harkokin tattalin arziki mai alaka da teku daga ma’aikatar sufuri.
Shugaban ya mayar da Abubakar Momoh daga ma’aikatar matasa ta tarayya zuwa ma’aikatar raya Neja-Delta.
Sanarwar sauye-sauyen wadda ta fito ta hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labaru Ajuri Ngelale ta ce yanzu Bunmi Tunji-Ojo ya koma ma’aikatar harkokin cikin gida, Sa’idu Alkali kuma shi ne sabon ministan sufuri.
Bugu da kari, an mayar da Ministocin Ma’aikatar Man Fetur da Gas zuwa Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya inda Sen. Heineken Lokpobiri a yanzu shi ne ƙaramin Ministan man fetur, yayin da kuma Hon. Ekperipe Ekpo shi ne Karamin minista mai kula da ɓangaren 'Gas'.
Hotunan yadda aka rantsar da ministoci
No comments