Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yariman Gombe ya riga mu gidan gaskiya

  Allah Ya yi wa Yariman Gombe da ke Jihar Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, rasuwa. Ya rasu ne da maraicen Talata dab da sallar Magar...

 


Allah Ya yi wa Yariman Gombe da ke Jihar Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, rasuwa.

Ya rasu ne da maraicen Talata dab da sallar Magariba a gidansa da ke unguwar Tudun Wada a Gombe.

Marigayin ya rasu bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Kafin rasuwarsa, shi ne Yariman Gombe, kuma Babban Hakimin cikin garin Gombe da kewaye.

Kazalika, marigayi Baffa ne ga Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III.

Ya rasu yana da shekara 77 a duniya, ya bar matan biyu da ‘ya’ya 19.

Za a yi jana’izarsa a ranar Laraba da misalin karfe 2 na ranar a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar shehu Abubakar III.

No comments