Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

A Buɗe Iyakokin Ƙasar Nan Domin Shigo Da Kayan Abinci -Saƙon Gwamna Abba Kabir Yusuf Ga Tinubu

Daga Zailani Mustapha Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta duba halin yunwa da a...


Daga Zailani Mustapha

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta duba halin yunwa da ake ciki a Nijeriya da matsin rayuwa ta buɗe iyakokin Nijeriya domin a shigo da abincin daga ƙasashen waje. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyara ta musamman da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, CG Bashir Adewale Adeniyi, ya kai masa q gidan gwamnati da ke Kano.

A yayin ziyarar ta Kwanturola-Janar, gwamnan ya koka kan halin da ake ciki na yunwa a ƙasar nan sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Ya kuma yi kira ga Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta duba batun sake buɗe iyakokin ƙasar nan domin shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje domin rage raɗaɗin da ake fama da shi.

Sai dai gwamnan ya nuna gamsuwarsa da shirin da Hukumar Kwastam ta fara domin rabon kayan abinci ga al’ummar Kano, inda ya buƙace su da su tabbatar domin ganin wannan aikin alheri ya kai ga waɗanda abin ya shafa.

No comments