Da safiyar yau Talata 26/3/2024, al'ummar Unguwar Rimi dake cikin garin Kaduna suka fito zanga-zangar rashin jin daÉ—in su a...
Da safiyar yau Talata 26/3/2024, al'ummar Unguwar Rimi dake cikin garin Kaduna suka fito zanga-zangar rashin jin daɗin su akan yadda ake satar yara ƙanana a Unguwar wanda a shekaranjiya 23/3/2024 aka kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da satan yara.
Hami'an tsaron ƴan sanda na riƙe da waɗanda ake zargi. Sai dai al'ummar Unguwar sun nuna rashin jinɗaɗi akan yadda har zuwa yanzu babu wani mataki da aka ɗauka akan waɗanda ake zargi da satan yara.
Masu zanga-zangar sun je har ofishin ƴan sanda dake Unguwar inda suka riƙe kwali suna kira ga jami'an tsaro su yi gaggawar ɗaukar mataki akan duk wanda ake zargi da satan yara.
Ga wasu daga cikin hotunan da muka É—auko muku a yayin zanga-zangar.
📷Muhammad Rabeel Ismail
No comments