Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abin Da Yake Faruwa A Jihar Zamfara

Wasu mazauna garin Tsafe da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaidawa Madogara TV/Radio cewa; a jiya da daddare ne sai ga labari ...


Wasu mazauna garin Tsafe da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaidawa Madogara TV/Radio cewa; a jiya da daddare ne sai ga labari na yawo cewa daga wajen Kuncinkalgo an ga 'yan ta'adda suna fuskanto garin Tsafe. 

Ganau ya shaida mana cewa; "muna zaune a inda muke shan ruwa da salloli bakin kemist din 'yan'uwa sai ga harbe-harbe mun fara ji daga nan a nata guje-guje". 

"Ni kaina yanzu haka da gudun tsiya na iso gida", ya tabbatar mana. 

Rahotanni sun nuna cewa; idan ba a manta ba a shekaranjiya da dare ne kusan sha biyu, gamayyar 'yan ta'adda suka shiga garin na Tsafe inda suka kwashe awanni suna ruwan wuta kuma sun tafi da mutane da dama yawancin su ma'aikatan aikin hanya ne na kamfanin SETRACO mai aikin hanyar Zariya zuwa Gusau zuwa Sakkwato.

Sannan har wala yau ƴan ta'addan sun ƙone motar sojoji tare da motar 'yan sa kai na Askarawa da gwamnatin jiha ta ƙaddamar a kwanaki sannan sun kashe ɗaya daga cikin Askarawa da wani yaro sun jiwa wasu rauni yanzu haka suna karbar magani.

No comments