Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Neja ta yabawa ayyukan hukumar AcResal a jihar, kwamishinan ma'aikatar muhalli da yanayi...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnatin Neja ta yabawa ayyukan hukumar AcResal a jihar, kwamishinan ma'aikatar muhalli da yanayi, Hon. Yakubu Mohammed Kolo ne yayi yabon lokacin da tsohon shugaban hukumar Malam Usman Garba Ibeto yake mika takardar ajiye aiki ga sabon shugaban hukumar Malam Shehu Raji yammacin talatar makon nan a babban dakin taro na ma'aikatar ayyuka ta jihar Neja.
Tunda farko a bayanin, kwamishinan ya bayyana cewar ayyukan AcResal wanda hadin guiwa ne da bankin duniya ayyuka ne da suka zo daidai da kudurin sabuwar gwamnatin Hon. Umar Mohammed Bago na samar da sabuwar jihar Neja, wajen cigaban kasa da bunkasar tattalin arzikin jihar.
Hon. Kolo, ya nemi tsohon shugaban da ya shirya wa sabon aikin da gwamnatin jiha za ta bukace shi domin kwazonsa da jajircewa wajen neman shawarwari da irin dubarun da yayi anfani da shi wajen samar da gurabun ayyuka ga jihar kamar yadda ya taka rawa a baya, musamman lokacin da ya jagoranci shirin bankin duniya na Fadama, RAMS da UNDP da hukumar NEWMAP zuwa AcResal.
Tunda farko a bayaninsa, tsohon shugaban hukumar, Malam Usman Garba Ibeto, ya yabawa irin hadin kai da kwarin guiwar da ya samu daga ma'aikatar muhalli zuwa abokan aikinsa na hukumar AcResal, wanda shi ya ba shi kwarin guiwar da jihar Neja ta zamo a sahun farko da suka ci gajiyar ayyukan bankin duniya.
Tsohon shugaban wanda yake cika shekaru talatin da biyar a fagen aiki, yace a shirye yake wajen bada gudunmawarsa dan ganin duk wani cigaba da ake bukata jihar Neja na sahun gaba, musamman a kudurin gwamnatin na samar da sabuwar jihar Neja.
A bayaninsa, tsohon Darakta mai kula da ayyukan musamman na hukumar AcResal, wanda shi aka damkawa alhakin kula da hukumar a yanzu, Malam Shehu Raji, ya yabawa kwarin guiwar da ya samu da tsohon shugaban hukumar, a lokacin aikinsa.
Malam Raji, dukkan ayyukan da aka gudanar a baya akan idonsa aka gudanar da su, kuma zai tabbatar ya dora akan inda tsohon shugaban ya tsaya.
Ayyukan hukumar AcResal dai ayyuka ne na hadin guiwa tsakanin gwamnatocin jahohi da bankin duniya, kan inganta sauyin yanayi, da ya shafi yaki da kwararar hamada, samar da ingantaccen yanayi dan fadada kasar noma, taimakawa mutanen karkara wajen tsayuwa da kafarsu wajen kare muhallansu daga zaizayar kasa, ta hanyar karfafa guiwarsu wajen bunkasa kasar noma da tsaron muhallai daga barazanar ambaliyar ruwa.
Malam Usman Garba Ibeto, ya ce a rahoton da hukumar ta tattara zuwa yanzu akwai yankunan da ba su cigajiyar ayyukan hukumar saboda matsalar tsaro da wasu yankunan jihar ke ciki.
Ya ce batun sauya fasalin wasu ayyukan da suka shafi yankunan Mokwa da Rafin-gora yana kan tebur domin rahoton bankin duniya ta amince da shi.
No comments