Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar kula sauyin yanayi da ceto kasar noma daga barazanar zaizayewa (Agro-Climatic Resilience In Se...
Daga Awwal Umar Kontagora
Hukumar kula sauyin yanayi da ceto kasar noma daga barazanar zaizayewa (Agro-Climatic Resilience In Semi-Arid Landscape (ACReSAL) Project na yunkurin ceto hekta dubu ashirin dan martabar bangaren noma da samar da abinci inda ake sa ran kashe dala miliyan dari uku da hamsin a jahohi goma sha tara har da Abuja.
Kodinetan shirin ACReSAL na jihar Neja, Malam Raji Shehu Adam ne ya bayyana hakan a wani taron yini daya da ya gudana tsakanin masu ruwa tsaki da kwararru inda ake yunkurin ceto hekta dubu ashirin.
Shirin wanda na gwamnatin Neja bisa hadin guiwar ma'aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi, ma'aikatar gona da ma'aikatar ruwa da kula cigaban manyan magudanan ruwa na jiha, wanda shiri ne na majalisar dunkin duniya da FAO.
Da yake bayani, Project Coordinar, Malam Raji Shehu Adam yace manufar hukumar shi ne samar da kyakkyawar yanayin aikin gona dan ceto rayuka. Wanda ya shafi yaki da zaizayar kasa, da kuma inganta dazuka wajen yin anfani da su dan samar da abinci da samar da kudaden shiga ga al'umma.
Raji ya ce sakamakon zaizayar kasa a unguwar Hausawa hukumar na sa ran ceto hekta takwas, yayi da Babban Rami hukumar na sa ran ceto hekta takwas wanda a wannan bangaren kawai ana sa ran ceto hekta goma sha shida dan bunkasar noma da samar da abinci.
ACReSAL ta bayyana cewar a wannan shekarar za ta mayar da hankali ne akan wadannan muhimman aikin guda biyu dan ganin jihar ta cigaba da rike kambunta wajen zama sahun gaba, wanda muna kyautata zaton zamu kammala aikin ceto kasar daga barazanar zaizayar, wanda aikin hadin guiwa ne tsakanin mu FAO wanda za a ceto sama hekta dubu dari uku a jahohi sha tara har da Abuja.
Hukumar na bukatar tallafawa mutane miliyan 3.4 wanda mafi yawa ana son su kasance mata ne daga cikin dala miliyan dari uku da hamsin da aka ware a matsayin rance ga al'ummar da abin ya shafa, a yankunan jahohi goma sha tara har da Abuja.
Hajiya Rabi Mamman Lafiya daya cikin jagoran shirin da ke aiki da hukumar ACReSAL tayi karin haake akan matakan da za a bi wajen cin anfanin wannan shirin. Wanda kungiyar manoma da samar da abinci na United Nation ( FAO) ta sanyawa hannun a cikin watan Nuwamba na 2023.
Ta bayyana cewar daga cikin kudurin hukumar mu shi ne ceto kasa daga barazanar zaizaya ta yadda gwamnat za ta samu nasarar cin ma burinta na karfafa guiwar manoma da samar da ayyuka ga jama'a.
Acewarta mu ka zabi hekta da bai wuce hamsin zuwa dari ba a kowani karkara musamman idan mun samu rahoto, muna yin kwalbati, samar da filin noma da kiwo.
Hukumar kan tallafawa mutanen yankin da tallafi dan samun abin yi, shirin da ake sa ran fara shirye shiryen cikin watan Afrilu na 2024 ya kuma fara gudana daga watan May zuwa July wanda ya kunshi kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara, Paikoro da Bosso, wanda an cire kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi sakamakon matsalar tsaro.
A bayanin kwamishinan gona, Hon. Musa Bawa Bosso, yace yanzu haka gwamnatin jiha ta samar da taraktocin noma sama da dubu daya wanda yanzu haka an fara horar da ma'aikata da kula da taraktocin, saboda wanda ke da kuduri yana iya bayyana wa ma'aikatar dan ba shi damar yin aiki da kayan noma da gwamnati ta tanada.
Hon. Yakubu Mohammed Kolo, kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi, yace kudurin hukumar nan a jihar Neja abin a yaba ne, domin gwamnati ta himmantu wajen dawo da martabar noma dan samun dogaro da kai da abinci wanda gwamnatin tarayya ta yaba wa manomi gwamna Umar Mohammed Bago, wanda tabbas duk wani goyon bayan da hukumar nan ke bukata gwamnatin Neja a shirye take ta ba ta.
Daga cikin kwamishinonin da suka halarci zaman sun hada da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, kwamishinan ma'aikatar gona, Hon. Musa Bawa Bosso, sai kwamishinan ruwa da kula da manyan tafkuna, Hon. Yahaya Alhassan Gwagwa, da kwamishinan kudi, Hon. Lawal Maikano.
No comments