Daga Nuruddeen Isyaku Daza Gwamnatin Jihar Neja ta haramta Sukuwar doki a cikin ƙwaryar garin Minna, babban Birnin jihar. A wan...
Daga Nuruddeen Isyaku Daza
Gwamnatin Jihar Neja ta haramta Sukuwar doki a cikin ƙwaryar garin Minna, babban Birnin jihar.
A wani jawabin da Limamin Tsalle ÆŠaya ya tattaro daga ofishin Mai Girma Gwamna Umaru Mohammed Bago na cewa duk wanda aka kama da laifin take dokar zai É—anÉ—sna kuÉ—arsa.
Gwamnatin ta bayyana wasu wuraren da aka ware na musamman na sukuwar dawakai da suka haɗa da: filin wasan polo dake tsohon filin jirgin sama kusa da sabon kasuwa Kure. Sai kuma fiin sukuwa na Sarkin yaƙi wanda ke kusa da Shakwata a kan hanyar Gwada.
Wannan umarni na zuwa ne ƙasa da ƴan sa'o'i kaɗan bayan da aka samu ɓarkewar rikicin Daba a yayin gudanar da hawan sukuwa na goman ƙarshen Azumi.
Gwamnan ya lashi takobin cewar, a ƙarƙashin kulawarsa ba zai taɓa lamuntar wasu ƴan tsiraru na hana al'umma sukuni ba, a don haka duk wanda yaƙi ji to baya ƙi gani ba.
No comments