Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rashin Kunya Ga Gwamna Uba Sani: APC Ta Dakatar Da Shugaban Mata Na Jam’iyyar

Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar mata na jam’iyyar saboda zarginta da yi wa gwamnan jihar Uba Sani rashin kun...

Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar mata na jam’iyyar saboda zarginta da yi wa gwamnan jihar Uba Sani rashin kunya da kalamai marasa ɗa'a a ƙoƙarinta na  goyon bayan tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Idan ba a manta ba, tun bayan caccakar gwamnatin El-Rufai da magajinsa Uba Sani ya yi masoya da magoya bayan ƴan siyasar biyu suka shata layi a tsakanin su a jihar.

Uba Sani ya bayyana a wajen taro a Kaduna a ranar Asabar cewa El-Rufai ya tattago basussuka a lokacin da yake gwamnan Kaduna da yanzu tarin bashin ya sa ko albashi ba ra iya biya.

Sai dai kuma shugaban mata na APC Maryam Suleiman, da aka fi sani da Mai Rusau ta maida wa gwamnan martani inda ta ce masa kuka bayan hari ya ke yi.

Maryam a wani martanin da ta yi ta gwaɓawa gwamnan magana, inda take cewa; "Tunda ka ce ba kuɗin da za ka yi aiki sai ka tarkata ka ƙara gaba, ka yi murabus kawai. Kuma ai da kai aka ciyo bashin kana kan gaba wajen ciyo bashin kuma yanzu ka zo ka ce wai ai babu kuɗi", in ji ta.

Bisa waɗannan kalamai ne Jam’iyyar ta dakatar da ita ta ce za ta gudanar da bincike akai.

Jaridar Madogara ta labarto cewa Jam’iyyar ta ce akwai hanyoyi da dama da ya kamata Maryam ta bi a jam’iyyance domin warware irin wannan matsala kamar yadda dokar jam’iyyar ta gindaya, ba kawai a hau shafukan sada zumunta ba a riƙa surutai ana yi wa gwamna rashin kunya da gwaɓa masa magana.

A wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban APC na gundumar da Maryam ta fito wato Badarawa/Malali, Alhaji Ali Maishago da Sakatarensa, Zakkah Bassahuwa, sun tabbatar da dakatar da ita daga jam'iyyar a ranar Lahadi 31 ga watan Maris ɗin 2024 bisa zargin ɓatawa gwamnan suna tare da gabatar da bayanai ga al'umma da ya shafi jam'iyyar ba tare da izini ba domin ɓatawa gwamna Uba Sani suna. 

Sun ce sun dakatar da ita har su kammala bincike a kan lamarin. 

No comments