Daga Awwal Umar Kontagora Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu sana'ar kabu kabu ( Motorcycle Operators Union Of Nigeria) ta ka...
Daga Awwal Umar Kontagora
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu sana'ar kabu kabu ( Motorcycle Operators Union Of Nigeria) ta kasa reshen jihar Neja, Comr. Shafi'i Ladan Maishera ya jawo hankalin yayan kungiyar wajen kaucewa daukar doka a hannun su a duk lokacin da matsala ta taso, domin yanzu sana'ar kabu kabu ta zamo halastacciyar sana'ar da gwamnati ta amince da ita, kan yasa aka yi mata rajista karkashin dokar sana'o'i ta kasa mai zaman kan ta.
Wajibi ne duk wani dan kabu kabu ya tabbatar yana bin dokokin hanya, da biyan kudin haraji ga gwamnati dan karawa gwamnati kwarin guiwa wajen sauke nauyin da ke kan ta.
Duk wasu matakan da ya kamata mu dauka a dokance muna bin sa dan ganin ba mu sabawa dokokin kasa ba
Sana'ar kabu kabu, sana'a ce ta rufin asiri da ya kamata mu mutunta kamar yadda gwamnati ta mutunta mu, dan haka muna da kwarin guiwa tunda gwamnatin da ta amince da mu ta daga darajar mu har tai mana hadaka da kungiyar kwadago ta kasa, ta irin alfanu da muke da shi wajen samar da gurabun ayyuka ga al'umma da kuma anfanu wajen samar da kudaden shiga gare ta.
Dan haka a shirye MOUN take wajen ganin ta kyautatawa yayanta, wajen kare mutuncin su, da taimaka masu a duk lokacin da matsala ya same su.
Dan haka, mu kiyaye dokokin tuki da na hanya, mu daina yawan gudun wuce haddi akan ababen sufurin mu, kuma mu kiyaye rayuka da lafiyar fasinjojin mu da na sauran jama'a, hakan zai taimaka gaya taimakawa jami'an tsaro da jami'an hanya wajen rage yawaitan hadurra da ke da alaka da tukin ganganci.
Shugaban, ya jawo hankalin masu sana'ar kabu kabu musamman a wannan lokacin bukin sallah karama mai zuwa, da su kaucewa tunkin ganganci da sunan murnar bukukuwan sallah, domin rai da lafiya suna muhimmanci gaya wajen cigaba da karuwar tattalin arzikin kasa, inji shi.
No comments