Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kashe Matasa Biyu Bisa Zargin Ɓarayin Babura Ne A Zariya

Daga Idris Umar, Zariya A cikin satin da ya gabata ne al'ummar garin Samaru dake karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna mur...


Daga Idris Umar, Zariya

A cikin satin da ya gabata ne al'ummar garin Samaru dake karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna murnar su ta koma ciki.

Abin ban tausayi shi ne wayewar garin Litinin ƙarshe na azumin bana da ya yi daidai 8/4/2024 aka tsinci gawarwakin wasu matasa guda biyu sanannun a garin Samaru.

Matashin na farko sunan shi Suleiman Usman, ɗan shekaru 25.

Sai na biyu mai suna Adamu (Faka-Faka) ɗan shekaru 30 duk a tsinci gawarsa ne a wata gona dake kusa da garin Basawa hanyar Hunkuyi duk a ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Bayan iyayen ƴaƴan sun nemi ƴaƴansu sun gaji ne sai labari ya watsu a cikin gari cewa an kashe wasu ɓarayin mashin har an banka masu wuta a hayar Hunkuyi.

Hakan yasa 'yan sandan yankin suka binciki inda gawar ta su take don ɗaukar matakin bincike.

Bayan 'yan sandan sun adana gawar a mutuware ne da kwana ɗaya sai labari ya canza kamar haka.

Iyayen Suleman da iyayen (Ado Faka-Faka) sun ce ƴaƴansu ba ɓarayi bane an kashe sune bisa rashin sani sun je ɗiban maganin sanyi ne.

Hakan yasa waƙilinmu ya tuntuɓi mai magana da bakin iyayen wanda aka kashe wato Malam Ubale.

Malam Ubale ya bayyanawa manema labarai cewa ƴaƴansu sam ba ɓarayin mashin bane bisa haka ne suka nemi dama ga hukumar 'yan sanda yankin cewa su ba su gawarwakin ƴaƴansu su yi musu sallah kuma suna godiya an ba su ƴaƴansu yanzu haka an yi musu jana'iza kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Bayan haka malam Ubale ya ce kamar yadda aka san ɗaya daga cikin wanda ake zargin mai suna Ado Faka-Faka shi yana sana'ar bayar da maganin gargajiya ne wanda hakan yasa ya haɗu da abokinsa Suleman suka je ɗibar magani cikin dare in da a can ne suka gamu da ajalinsa ta hanyar yin masu sara da Gatari na rashin mutunci da nufin ɓarayi ne su. 

Malam Ubale ya ce su ƴaƴansu ba a taɓa kama su da wani laifin sata ba don haka duk wanda ya yi musu wannan hukunci Allah zai masu sakayya, in ji shi.

Bincike ya nuna cewa ya zuwa yanzu babu wanda yasan wanda ya kashe matasan guda biyu.

Amma wata majiyar ta ce tabbas matasa sun taka sawun  ɓarawo ne a wannan dajin da aka daɗe ana fakon wasu mutane masu ƙwacewa mutane babura.

Waƙilinmu ya tuntubi mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Kaduna ASP Mansur Hasan akan lamarin amma ya ce, da yake abin ya faru ne a lokacin hutun sallah amma za su binciki lamarin kuma za su sanar da halin da ake ciki da zarar sun sami tabbacin yadda abin yake.

Bincike ya tabbatar da cewa ba wannan bane na farko da aka kashe mutum bisa zargin satar babura a garin na Samaru don haka jama'an garin suke kira ga hukuma da a ɗauki matakin wayar da kan jama'a don kaucewa kashe ran Ɗan Adam babu wani dalili mai ƙarfi na yin kisan.

Ya zuwa yanzu babu wani mutum ko wata hukuma ko ƙungiya da ta amsa yin kisan matasan guda biyu amma dai ana ta Allah-wadai da faruwar lamarin.

No comments