Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NPA Ta Karbo Bashin Dala 700 Daga Bankin Citibank Domin Gyara Tashar Jiragen Ruwa Na Apapa Da Tin-Can

Daga Bello Hamza, Abuja A halin yanzu Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, NPA ta kammala shirin karbo bashin Dala ...


Daga Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, NPA ta kammala shirin karbo bashin Dala Miliyan 700 domin gudanar da ayyukan gyare-gyaren a tashar jiragen ruwa na Apapa da Tin-can. Za a karbo bashin ne daga bankin Citibank tare da tallafin hukumar qasar Birtaniya ta ‘UK Export Finance (UKEF)’,

Haka kuma hukumar ta fara tattaunawa da wasu cibiyoyi domin samar da wasu kudaden dokin aikin gyara tashoshin ruwa na gabashin qasar nan da suka hada da na Kalabar, Warri, Onne da na riba tare da kuma sake gida wani bangare na ‘Escravos breakwater’.

A jawabinsa  ayyain snya hannu a kan yarjejeniyar bashin a ranar Laraba, shugaban hukumar NPA, Mohammed Bello-Koko, y ace, tuni aka tura wasikar neman amincewar ofishin shugaban mai kula da basuka (DMO).

Da zaran an samu kudin za a fara ayyukan da aka sa a gaba don bunkasa tashoshin jiragen ruwan ba tare da bata lokaci ba.

“A cikin shekara 2 da suka wuce ne muka fahimci bukatar sake yi wa dukkan tashoshin ruwan kasar nan kwaskwarimar da ya kamata. A kan haka muka bude hanyoyin samar da kudaden gudanar da aikin domin samun nasarar da ya kamata.

“A tatunawar mu, mun fahimci bukatar ware tashar jiragen ruwa na Legas daga sauran tashoshin jiragen ruwa na gabashin kasar nan, a kan haka muka bude fagen samar da kudade daga kafofin samar da kudade don mu fuskanci aikin gyaran tashoshin jiragen ruwa na gabashin Nijeriya,” in jj shi.

Ya kuma kara da cewa,  ka’idojin da Citibank ya sanya na bayar da bashin shi ne ya fi sauki ga NPA saboda karancin ruwa.

Tun da farko, shugabar bankin Citibank Nigeria Limited, Ireti Samuel-Ogbu, ta bayyana cewa, bankin ya shirya aiki tare da NPA da kuma gwamnatin tarayya don bunkassa tashoshin ruwan Nijeriya.

No comments