Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AFAN Ta Jaddada Goyon Bayan Ta Kan Ƙudurin Gwamnatin Neja Na Ƙarfafa Guiwar Manoma Milyan Ɗaya A Jihar

Daga Awwal Umar Kontagora Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Neja (All Farmers Association of Nigeria) ta jaddada g...

Daga Awwal Umar Kontagora

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Neja (All Farmers Association of Nigeria) ta jaddada goyon bayan ta kan kudurin gwamnatin Manomi gwamna Umar Mohammed Bago na karfafa guiwar manoma milyan daya a jihar ta yadda gwamnatin ke yunkurin samar da abinci a nahiyar Afrika.

Shugaban kungiyar AFAN a jihar Neja, Alhaji Shehu Yusuf Galadima ya bayyana hakan a taron shugabannin kungiyoyin manoma.da masu ruwa da tsaki da kungiyar ta kira kan shirye shiryen fuskantar damanan bana.

Shugaban yace a bana gwamnatin Neja na yunkurin noma kadada miliyan hudu wanda tuni shirye shiryen gwamnatin yayi nisa, wanda ta sha alwashin samar da wadataccen iri, da takin zamani da duk wani abinda manomi ke bukata.

Shehu Galadima ya yabawa gwamnan kan wannan yunkurin wanda idan an samu nasara ba samar da abinci kadai ba, gwamnatin za ta samar da wani sabon babi ne na kasuwancin abinci da zai baiwa baki daga kasashen Afrika damar shigowa jihar dan yin cinikayyar kayan abinci.
Da yake karin haske ga manema labarai, mataimakin shugaban kungiyar ta jiha, kuma sakataren kungiyar manoman auduga, kuma sjugaban manoman alkama haka kuma sakataren kungiyar manoman tumatur, Jakadan zaman lafiya, Amb. Nura Hashim yace wannan shirin zai gudana ne a karkashin shirin Niger FOOD wanda gwamnatin jiha ta kirkiro tare da hadin guiwar ma'aikatar gona da hukumar NAMDA.

Amb. Nura, ya cigaba da cewar gwamnatin ta zabi abinci kala goma da ta ke son karfafawa, wanda hakan yasa suka gayyato kodinetoci na kananan hukumomi ashirin da biyar da masu ruwa da tsaki da sauran kungiyoyin manoma dan yabawa gwamnatin jiha kan wannan yunkurin da ta ke neman goyon bayan manoman jihar.
Daga cikin kayayyakin abincin da gwamnatin ke kudurin mayar da hankali akan su ya kunshi shinkafa, masara, dawa, sai rogo da doya, ridi da waken suya, sauran sun hada da auduga da kuma wani nau'in waken suya.

Ya cigaba da cewar wannan tsari ne da aka kaddamar karkashin cibiyar Niger FOOD, wanda kula da harkar noma yana karkashin kulawarta, yayin da ma'aikatar gona da hukumar NAMDA zasu horar da manoma wannan sabon nau'in noman na zamani wanda ake sa ran noma hekta miliyan daya a jihar.

Dangane da matsalolin tsaro kuwa, mataimakin shugaban, yace gwamna Umar Mohammed Bago ya dauki matakin sanar da shugaban kasa halin rashin tsaro da wasu yankunan kananan hukumomi ke fuskanta, wanda gwamnatin tarayya ta sha alwashin dukkanin yankunan da ke fuskantar matsalar tsaro, gwamnati za ta bada ingantaccen kulawa a yankunan.
Abinda muke kokarin wayar da kan manoma shi ne su sani dukkanin wani abinda za a bayar rance ne kuma dole sai an biya, dan haka wajibi kowace karamar hukuma ta koma ta hada kai da sarakunan gargajiya na yankunan su domin duk mutumin da ba manomi ba ne ba zai anfani shirin ba.

Wani binciken wakilinmu ya gano cewar shirin mataki biyu ne, matakin farko shi ne na manyan manoma, duk abinda suka samu na riba za a yi raba daidai ne da gwamnati, yayin mataki na biyu, shi ne na kananan manoma, duk abinda suka noma zasu biya bashin daidai da abinda suka karba sauran abinda ya rage shi ne ribarsu.

AFAN, tace wannan shiri ne da gwamnatin jiha ta karbo bashin kudade dan aiwatar da shi, wanda wajibi bayan an girbe anfani gona an sayar za a mayar da kudin.
Amb. Nura yace kar manoma su ji tsoro domin ba wanda zai amshe masu amfanin gonarsu ko abin da suka noma, illa wata hanya ce da gwamnati ta kirkiro dan karfafa guiwar manoman jihar, ta sauya tunanin su daga noma abincin da zasu ci zuwa manoma anfanin gona zuwa kasuwanci, wanda muna san bayan kammala wannan shirin na noma kalolin abinci goma za a fadada zuwa wasu nau'ukan abinci da kasuwar duniya ke bukata.

Saboda sauran kungiyoyi da ke noma sauran nau'ukan abinci da su shigo cikin wannan shirin, hakan zai karfafa guiwar gwamnati wajen fadada shirin a gaba.
Malam Garba Ibrahim, shugaban kungiyar masu safarar kayan abinci na gwamnatin tarayya yace idan aka samu nasarar shi, jihar Neja za ta zama ta farko da yan kasuwa za su yi gogoriyon zuba jarinsu a harkar abinci da za a samu saukin samun nau'ukan abinci da za rika fitarwa waje.

No comments