Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyyar Zahra Relief Ta Kammala Shirin Rabon Kayan Abincin Buɗa-baki

Daga Zailani Mustapha Kamar yadda suka saba a duk shekara, Gidauniyyar Zahra Relief na gudanar da ayyukan raba abincin buɗa-baki...


Daga Zailani Mustapha

Kamar yadda suka saba a duk shekara, Gidauniyyar Zahra Relief na gudanar da ayyukan raba abincin buɗa-baki ga al'ummar musulmi a watan Ramadan, a bana ma ba su ƙasa a guiwa ba, inda suka tsunduma a wannan aiki na tsawon kwanaki kusan 10 a birnin Tarayya Abuja. 

Wakilinmu ya labarto mana cewa: rabon abincin buɗa bakin ya soma gudana ne a ranar 16 ga watan Ramadan 1445, inda aka kammala shi a ranar 24 ga watan. 

Dubban al'umma ne da suka fito daga Unguwannin Jabi, Garki, Utako, Life Camp dake birnin Tarayya Abuja suka amfana da wannan tallafin. 

Abdurrahman Muhammad, ɗaya daga cikin wanda suka jagoranci rabon abincin buɗa-bakin ya shaidawa wakilinmu cewa; maƙasudin raba abincin buɗa-bakin shi ne; "domin sauƙaƙawa zuwa ga mabuƙata a cikin al'umma ba tare da rarrabewa ba,  kamar yadda yake a tsarin gidauniyar na yin ayukkan jinƙai da taimakon mabuƙata da gajiyayyu", ya tabbatar. 

Da yawan waɗanda wakilinmu ya samu tattaunawa da su sun nuna jinɗaɗinsu da nuns gamsuwa da wannan tallafin dafaffen abincin da ake ba su a kowacce rana a daidai lokacin buɗa-baki inda suka yi wa gidauniyyar addu'ar samun nasara a dukkan ayyukanta tare da yi mata fatan alheri. 

Shirin tallafin abincin buɗa-bakin ɗaya ne daga cikin ayyukan gidauniyyar, kuma suna yin hakan ne da nufin rage wa al’umma wahalhalun da suke sha musamman wajen samun abin da za su ci a yayin da al’ummar ƙasarnan ke ci gaba da shan wahala sakamakon tashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi. 

No comments