Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bijilanti A Jihar Neja Ta Sha Akwashin Tabbatar Da Matsayin Gwamnati Kan Kawar Da ‘Yan Sara Suka A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar 'Nigeria Vigilantee Security Cops ( NVSC)' reshen jihar Neja ta sha alwashin kawar da...



Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar 'Nigeria Vigilantee Security Cops ( NVSC)' reshen jihar Neja ta sha alwashin kawar da duk wanda ta samu yana yawo da makami a Minna. 

Shugaban rundunar Kwamanda Nasiru Mohammed Manta ne ya bayyana hakan yammacin Litinin din makon nan, bayan wani zama da majalisar dokokin jihar Neja ta yi kan sabon kudurin doka na hukunta iyayen da ke zuwa karban belin 'ya'yan su da aka samu da laifin ta'addanci 

Kwamanda ya ce rundunar 'Vigilantee' a shirye take wajen tabbatar da wannan hukuncin, domin umurnin gwamna ne kuma hakkinsa ne kare rayuka da dukiyoyin al'ummar da suka zabe shi.

"Saboda haka ban baiwa iyayen yan ta'adda shawara kuma bai ce su ajiye makami ba, duk wanda muka yi a rangama da shi zai ga aika aika domin matsayinsu daya da yan ta'adda, duk mutumin da ya yi amfani da makami don zubar da jinin wani tare da yin sata wallahi idan ya fada komar mu zai ga ba daidai ba. Idan mutum ya tsira mu mika shi ga rundunar yan sanda, idan kuma kwanan shi ya kare mu kawar da shi.

"Ina jaddada ma al'ummar jihar Neja, mai girma gwamna a shirye yake kuma yana bai wa rundunar kwarin guiwa na kayan aiki na tabbatar da aiki na gudana ba tare da tangarda ba, kuma wannan kudurin doka da majalisar dokokin jihar Neja ke shirin gabatarwa rundunar tsaro a jihar nan za su samu kwarin guiwar gudanar da ayyukan su dan kare rayuka da dukiyoyin jama'a kamar yadda hakkin ya rataya a wuyansu.

"Matsalar sara suka na ciwa al'ummar Minna tuwo a kwarya wanda kusan duk yan ta'addan da ake kamawa cikin gari Minna da laifin kisa da satar dukiyoyin jama'a bayan kwana biyu sai jami'an tsaro su sako su sakamakon matsin lambar da suke samu na wasu boyayyun fuska, wanda ana kyautata zaton wannan sabon dokar zai bada damar cafke duk wani da ya boye ya tafi neman belin wani mai laifi", ya tabbatar.

No comments