Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NAFDAC Ta Ƙwace Jabun Kayayyaki Da Kuɗinsu Ya Kai Naira Miliyan 50 A Kantunan Abuja

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta kai samame a manyan kantunan babban birnin Najeriya Abuja, inda t...



Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta kai samame a manyan kantunan babban birnin Najeriya Abuja, inda ta ƙwace jabun kayayyakin da dama.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce sun kai samamen ne a kasuwannin Garki, Wuse, Utako, Kugbo, Nyanya, da kuma Mararaba, inda suka kwace jabun kayan kwalliya da magunguna.

NAFDAC ta ce ta gano jabun kayan kwalliya tare da kama su a Shagunan Sahad, H-Medix, da kuma kasuwanni daban-daban, yayin da aka ƙwace jabun magunguna kuma a kasuwar Utako.

Sauran kayayyakin da hukumar ta ƙwace sun haɗa da mayukan shafawa na NIVEA, abubuwan tsabtace bayan gida na Harpic, da kuma turaren kamshi na ɗaki.

NAFDAC ta ce kuɗin jabun kayayyakin da ta ƙwace ya kai Naira miliyan 50, inda ta ce kuɗin mayukan shafawa na NIVEA kaɗai ya kai Naira miliyan 45.

Mista Embugushiki-Musa Godiya, shugaban sashen bincike na hukumar a birnin Abuja, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake sayar da kayayyakin da ba su da inganci, musamman ma jabun mayukan shafawa irin NIVEA da ake sayarwa da tsada fiye da na kayayyakin da aka amince da su.

"Waɗannan jabun kayayyaki na da illa sosai ga lafiyar lafiyar jiki, akwai yiwuwar kamuwa da cutar daji, da lalacewar koda, da kuma fatar jiki," in ji shi.

Hukumar ta sake jaddada aniyar ta na kawar da jabun kayayyaki da kuma kare lafiyar al’umma.

No comments