Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AGAFPAMA Da Kamfanin Kawaji Sun Sha Alwashin Bada Tallafi Ga Ƙananan Manoman Ƙasar Nan

Daga Awwal Umar Kontagora Hadaddiyar ƙungiyar manoma ta ƙasa (All  Green Agro Field Farmers) ta sha alwashin hada guiwa da kamfa...

Daga Awwal Umar Kontagora

Hadaddiyar ƙungiyar manoma ta ƙasa (All  Green Agro Field Farmers) ta sha alwashin hada guiwa da kamfanoni da gwamnatoci dan samarwa manoma walwalar zai karfafa su ga mayar da hankali a harkar noma. Sakataren kungiyar ta kasa kuma shugaban kungiyar a jihar Neja, Amb. Dr. Nura Hashim (Magakin sardaunan Hausa) ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga shugaban kamfanin Kawaji Enterprises, kamfanin da ke samar da kayan noma a arewacin kasar nan, Alhaji Shu'aibu Aliyu da ya ziyarci sakatariyar kungiyar larabar makon nan.

Amb. Nura Hashim, ya cigaba da cewar manufar kafa kungiyar nan, tallafawa manoma, ta hanyar samar masu da kayan aikin gona cikin saukin farashi, horar da su dubarun noma irin na zamani, dan tabbatar da samun ilimin aikin gona a saukake.

Sakataren, yace kofar mu a bude take ga duk wani kamfani ko hukuma da zai bada gudunmawa wajen bunkasa harkar noma, saboda haka za mu tabbatar mun shiga yarjejeniya da wannan kamfanin na Kawaji Enterprises dan samar da kayan aikin noma cikin saukin farashi ga dukan manomin da ya nemi hada guiwa da mu.
A bayanin shugaban kamfanin, Alhaji Shu'aibu Aliyu, yace kamfaninsa a shirye take wajen karfi da karfe da kamfanonin da ke samar da kayan aikin gona ciki da wajen kasar nan.

Shugaban, yace a shirye kamfaninsa ta ke wajen daukar dawainiyar duk wani horarwa ga manoma domin samun cikakken ilimin aikin gona.

Kamfanin Kawaji Enterprises tayi murna da farin cikin samun ire iren wadannan kungiyoyi masu kishi da son cigaban manoma.

No comments