Gidauniyar Zahra Relief Foundation na miƙa saƙon jajantawa bisa ibtila'in haɗarin motar gas da ya afku a babbar hanyar Karu ...
Gidauniyar Zahra Relief Foundation na miƙa saƙon jajantawa bisa ibtila'in haɗarin motar gas da ya afku a babbar hanyar Karu da ke Abuja a daren ranar Laraba.
Rahotanni sun tabbatar da asarar rayuka da dukiyoyi, a yayin da adadi mai yawa suka samu raunuka.
"Muna jajantawa ga iyalai, ƴan uwa da duk wanda abin ya shafa", in ji sanarwar gidauniyyar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; "Zahra Relief Foundation na kira ga al'umma da su nuna aikin jinkai ga wanda wannan ibtila'i ya shafa ta hanyoyin da za su iya riskar su. Haka kuma, muna kira kan bayar da tallafin jini ga masu hali domin ceto rayukan wanda suka samu rauni, bisa koyarwar musulunci na isar da hannun taimako.
"Asibitotan da ake iya bada gudunmawar jini, kamar yadda rahotanni suka nuna, sun haɗa da: National Hospital Abuja da Karu General Hospital, ko kuma a tuntubi Hukumar Bayar da Jini ta Ƙasa a lambarsu 07088370905 ko hanyar da mutum zai iya bi", sanarwar ta nusasshe.
"Muna rokon Allah SWT Ya ba wanda suka jikkata lafiya, Ya mayar da alheri ga wanda su ka yi asara. Allah Ya kiyaye afkuwar hakan", ta ƙarƙare.
No comments