Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

APC ta yi taka tsantsan idan ba haka ba wankin hula na iya kai ta dare a babban zaben ƙasa mai zuwa - Wana

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar turbar da ake tafiya yanzu a APC na rarrabuwan kawuna da ficewar da yayan jam'iyy...

Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar turbar da ake tafiya yanzu a APC na rarrabuwan kawuna da ficewar da yayan jam'iyyar APC ke yi zuwa wasu sabbin jam'iyyu, idan ba a yi a hankali a babban zabe mai zuwa wankin hula zai iya kai jam'iyyar dare. Dan kwamitin dattijai na zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben da ya gabata, Alhaji Awaisu Giwa Wana ne ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci kan ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i da wasu jiga jigan jam'iyyar da ake kyautata zaton su ma suna kan hanyar canja sheka.

Irin wannan iftila'in da ya faru da tsohon shugaban kasa Ebele Jonathan, wanda abinda ba a yi tsammanin faruwarsa ba, na amshe mulki hannun mai mulki ya faru kuma wannan kasawa ne kuma abin kunya ne.

Ya kyautu, shugaban kasa Bola Tinubu ya ajiye ra'ayinsa ya dawo kan ra'ayin jama'ar da suka wahala da shi kuma suka tallata shi har ya samu nasarar da ya ba shi ikon shugabantar kasar nan.

Awaisu Wana, ya cigaba da cewar akwai bukatar a kafa kwamitin dattijai dan saurare shakuwar kowa, a yafe wa juna a tabbatar ba a samu matsala a zabe mai zuwa ba.

Duk wanda yace arewa ba ta da tasiri a siyasar kasar nan yayi kuskure babba, duk da rashin kishi da hadin kan da ake ganin manyan arewa na da shi, ba yadda za ka iya samun nasarar zabe muddin ba ka samu kuri'ar yan arewa ba.

Amma hanyar da ake tafiya yau, su kan su gwamnoni suna raka shugaban kasa ne amma ba sa tare da shi, saboda makusantar shugaban kasa su farka da wuri daga igiyar mulkin da ke rudarsu yanzu, kafin lokacin da zasu zo suna zargin junansu akan rashin gayawa juna gaskiya.

Ya kamata su El-Rufa'in nan da tawagarsu, a zauna dan dawo da su, domin dukkanin masu tunzuri a yau ba wanda ya bada gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben da ya gabata.

Dattijon, yace akwai kurakurai kuma akwai matsalolin da ya kamata a walwale su tun kafin lokaci ya kure, akwai kabilanci, akwai rashin adalci wajen rabon mukamai a gwamnatin nan, bai kamata wadanda suka hau tudu da gangare suka taka rawar ganin kafuwar gwamnatin nan a yi watsi da su kuma ayi tsammanin idan lokacin zabe yazo zasu sake maimaita kurakuran da suka tafka a baya ba.

Giwa Wana, ya jawo hankalin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Injiniya Abdullahi Umar Ganduje, da yayi anfani da kwarewarsa ta siyasa, ya tabbatar ruwan dufana bai lakume jam'iyyar APC ba a lokacin jagorancin shi ba.

No comments