Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mu kyautata Ibadarmu tare da yi wa shugabanni addu'o'in alheri - Sheikh Masha'Allahu

Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga al'ummar musulmi da su kyautata Ibadarsu wajen yawaita neman gafarar Allah, karatun ...

Daga Awwal Umar Kontagora

An yi kira ga al'ummar musulmi da su kyautata Ibadarsu wajen yawaita neman gafarar Allah, karatun Al-qur'ani mai tsalki da yawaita kyawawan ayyuka tare da yiwa shugabanni da kasa addu'o'in alheri.
Babban mai baiwa gwamna shawara akan harkokin shari'a kuma shugaban kungiyar masu fadakar masu aikin Umrah da aikin Hajji a jihar Neja, Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu ne yayi kiran bayan kammala tafsirin Al-qur'ani mai tsalki ranar sha takwas ga watan ramadan a masallacin hukumar kula da harkokin addini ta jihar Neja.

Masha'Allahu, ya cigaba da cewar maigirma gwamna Umar Mohammed Bago ya tara malamai da shugabannin kungiyoyin addini kan shirye shiryen watan ramadan, inda ya bayyana tsarin ciyarwa da rage farashin kayan abinci dan talakawa su samu sauki, tare da yin tsinuwa ga duk wadanda suka karkatar da kayan abincin.

Amma duk da hakan wadansu suka yi kukan kura suka aiwatar da son zuciyarsu, to mu ba mu tsine masu ba, amma su sani duk wanda ke da hannu wajen hana wannan aikin alherin Allah na ganin shi kuma baya bacci.

Jama'a su sani dukkanin kungiyoyin da aka umurta su bada na su tsarin dan tafiyar da wannan muhimmin aikin na alheri sun bayar amma dai ba mu san inda gizo ke sakar ba, domin gwamnati ba ta kira mu tace ta janye wancan tsarin ba, sannan ba a sake tara mu an bayyana mana sabon tsarin da ake tafiya a akai yanzu ba.

Duk da haka, muna jawo hankalin al'ummar musulmi da su sani wannan azumin da suke yi dan Allah su ke yin shi, kuma duk wani halin da suke ciki da sanin Allah, dan haka su tsalkake zuciyarsu wajen aikin Ibadah bisa ikhlasi.
Mu yaiwata istigfari, salatin Annabi da karatun Al-qur'ani mai tsalki tare da yiwa kasa da shugabanni addu'o'in samun nasara.

Kamar jiya muka fara azumin nan, da taimakon Allah duk da halin rashin kudi da matsin da jama'a ke ciki ga ramadan na gangarawa, to mu sani kwanakin mu ne ke gangarawa wanda duk ya tafi daga cikin adadin kwanakin numfashin mu ne ya rage, dan haka mu gaggawa wajen ayyukan alheri, mu sani walwala da jin dadi, ko kuncin rayuwa dukkansu daga Allah ne, kuma shi yasan tanadin da yayi muna akan wannan jarabawar.

No comments