Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jam'iyyar NNPP ta shirya shiga zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Jam'iyyar NNPP a jihar Neja ta bayyana cewar ta shirya dan shiga zaben shugabannin kananan hukumom...

Daga Awwal Umar Kontagora

Jam'iyyar NNPP a jihar Neja ta bayyana cewar ta shirya dan shiga zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da ake shirin gudanarwa karshen shekarar nan. Shugaban jam'iyyar Hon. Awwal Mohammed Goma ne ya bayyana hakan a wani takardar manema labarai da ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai yammacin larabar makon nan.

Hon. Goma, ya cigaba da cewar mun gamsu da tsare tsaren hukumar zabe ta jiha, dan haka ne muke da kwarin guiwar shiga zaben nan mai zuwa, saboda mun bi matakan da suka dace wajen fitar da yan takara kuma mun hori shugabannin jam'iyya daga matakin karamar hukuma zuwa mazabu su tabbatar sun yi adalci wajen tsayar da yan takarar da jama'a suka nuna bukatarsu zuwa gare su.

Dan haka, maganar hadaka da wata jam'iyya, muna da yakinin mulki na Allah kuma gare shi muke nema, ba mu ra'ayin hadin guiwar tsayar da yan takara da wata jam'iyya ko janyewa ma wani dan takarar ba dan NNPP ba ne.

Kamar kowace jam'iyya, muna cigaba da tattara sunayen yan takarar kafin wa'adin da hukumar zabe ta sanya na mika sunayen yan takara kafin fara yakin neman zabe, saboda mun shirya akan duk wani kafar ungulu da jam'iyya mai mulki za ta yi dan ganin jam'iyyun adawa ba su kai labari ba.

Ya kamata, al'ummar Neja su falka, yau shekara daya da watanni goma da jam'iyyar APC ta kafa mulki a jihar nan, amma ba wani muhimmin abu da talakan Neja zai nuna da sunan cigaban da gwamnatin Neja ta kawo.

Takardar ta cigaba da cewar duba da muhimmancin gwamnatocin kananan hukumomi ga talaka,yasa muka ga dacewar fito da yan takara masu kishi, masu akidar son cigaban jihar nan dan kafa harsashen da zai zamo silar fitar da jihar nan daga halin da suke ciki na rashin cigaba da dambarwar mulki, wanda duk wani da ya san cigaba ya dubi jihar Kano yasan cewar jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso duk da sara da sukar da yake sha ya kafa harsashen ceto jihar Kano daga hannun yan jari hujja.

Dan haka, muna kiran talakawan jihar nan, da su cire tsoro su yi abinda ya dace, domin tsarin shugabancin siyasa, tsari ne na jama'a dan jama'a kuma wanda jama'a suka zaba da hannun su.

Ina jadaddawa yayan jam'iyyar NNPP cewar shugabancin mu a jihar Neja zai tabbatar ya tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin al'ummar jihar da tabbatar da tafiya irin ta cigaba, wadda zai anfani jiha da kawo cigaba mai dorewa.

Ba ma gidoga, kuma ba mu yarda da gidoga ba, za mu tafi bisa tsarin dokokin jam'iyya dan tabbatar da kowani dan jam'iyya ya gamsu da irin salon shugabancin mu. Dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar za mu tsayar da yan takarar shugabancin kananan hukumomi zuwa kansuloli dan nuwa duniya NNPP ta zo kuma ta tsaya da kafarta a jihar Neja.

Dole mu fito mu yi gwagwarmayar siyasa, kamar yadda muka ji gwamnatin Neja ta sahalewa mata takarar mataimakan shugabancin kananan hukumomi daman wannan tsarin mu ne NNPP ta riga malam masallaci.

Muna kiran al'ummar Neja da su fito dan kare kuri'unsu wajen yin gwagwarmayar ganin ba a danne masu zaben su ba. Mun ga irin salon siyasar jagoran siyasar Kwankwasiyya, siyasar yanci da rashin nuna bambanci tsakanin talaka da mai kudi, tare da tabbatar da tsarin baiwa kowa damar samun ilimi dan cigaban rayuwa da bunkasar tattalin arzikin kasa.

No comments