Daga Awwal Umar Kontagora A daidai lokacin da hukumar zabe ta jihar Neja ke fitar da jadawalin zabukan kananan hukumomin jihar, gwamna Umar...
Daga Awwal Umar Kontagora
A daidai lokacin da hukumar zabe ta jihar Neja ke fitar da jadawalin zabukan kananan hukumomin jihar, gwamna Umaru Bago ya jawo hankalin jam'iyyar APC mai mulki kan cewar tsayar da dan takara bisa yarjejeniya yafi muhimmanci akan gudanar da zabukan fidda gwani wanda aka saba da shi.
Gwamnan yace duk mai sha'awar takarar kujerar karamar hukuma, ko kansila yana da hurumin sayen fom dan nuna sha'awarsa ga yin takarar kuma idan ya saye ya cike ya mikawa sakatariyar jam'iyya, saboda wannan shi ne tsarin doka.
Gwamnan a wani tattauna da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC ya hore su da jin tsoron Allah wajen fitar da dan takara, kuma sauran yan takarar da suka nuna sha'awarsu ga yin takarar kuma suka shiga cikin sulhu na marawa mutum daya, da su yi shi da kyakkyawar niyya.
Da yake karin haske ga manema labarai, littinin din makon nan, jigo a jam'iyyar APC, Alhaji Hamza Yanga Buba, yace lallai gwamna Umaru Bago ya yi kyakkyawar tunani na baiwa jam'iyyar APC mai mulki wannan shawarar.
Yanga, ya cigaba da cewar halin da matasan mu ke ciki na Sara -suka, wannan zai taimaka wajen dakile masu yunkurin yin anfani da zabukan fidda gwani ta hanyar yakin zabe ko wani abu makamancin hakan dan cin ma mummunar kudurinsu.
Sai dai, ina bada shawarar cewar idan mutum yayi yunkurin yin takara bai samu damar hakan ba ya kai shi ga canja sheka zuwa wata jam'iyyar, kuma saboda cancantarsa ya samu tikitin takara, idan ya ci zaben shi a ba shi, wannan shi ne adalci.
Dattijon, ya jawo hankalin dukkanin wadanda suke sha'awar tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomi, da kar su nauyin guiwa, su tabbatar sun shiga wannan takarar domin shi zabe abu yake haifarwa, nasara ko akasin shi kuma dukkanin su suna anfanar da dan siyasa.
Yanga, ya shawarci jam'iyyun adawa a jihar Neja, da su marawa gwamnatin jiha wajen ganin an gudanar da wannan zaben lafiya, domin hadin kai, goyon baya shi zai kawo mana cigaba da baiwa jam'iyyun adawa damar samun tagomashi da iya cin zabe.
No comments