Daga Awwal Umar Kontagora Majalisar sarkin Sasa Ibadan kuma Sardaunan Yamma, Alhaji (Dr.) Ahmad Haruna Maiyasin Katsina II, ta karrama Talla...
Daga Awwal Umar Kontagora
Majalisar sarkin Sasa Ibadan kuma Sardaunan Yamma, Alhaji (Dr.) Ahmad Haruna Maiyasin Katsina II, ta karrama Tallafin Bosso Karami, Amb. Dr. Nura Hashim da sarautar Magayakin sarakunan arewacin mazauna jahohi sha bakwai.
A takardar tabbacin nadin sarautar wadda majalisar sarkin Sasa shugaban majalisar sarakunan kudanci ta sanyawa hannu ta bayyana cewar sakamakon jajircewa wajen taimakawa marasa katfi, da jajircewarsa wajen bunkasa ga hadin kai tsakanin al'ummar Hausawa da sauran kabilun kasar nan, da cugaban matasa wajen zaman lafiya, da tsayuwa da kafarsu.
Sakamakon yasa masarautar ta ga dacewar wannan nadin na MAGAYAKIN jahohi sha bakwai na kudancin kasar nan. Majalisar tayi fatan sabon Magayakin zai amshi wannan karamcin da kyakkyawar zuciya hannu biyu tare da jajircewa wajen cigaba da wannan muhimmin aikin da ya somo tunda dadewa.
Majalisar tayi fatan alheri da wannan nadin,tare da fatar cigaba da aiwatar da kyawawan ayyukan hadin kai, zaman lafiya, cigaba da wayar da kan al'umma , musamman matasa wajen hadin kai, dogaro da kai wajen jajircewar neman na kai.
Da yake bayani ga manema labarai, ya yabawa majalisar sarkin Sasa, kuma Sardaunan Yamma na kudancin kasa bisa wannan karamcin, tare da tabbatar zai cigaba da jajircewa wajen wannan muhimmin ayyukan alherin da ya mayar da shi tubalin ginin rayuwarsa.
Tallafin Bosso Karami, yace wannan karamcin ba shi aka yiwa ba, an yi wannan karamcin ga matasan kasar nan musamman Hausawan Afrika.
Amb. Dr. Nura Hashim, wanda shi ne shugaban kungiyar Hadin kan Hausa da Hausawan Nijeriya da Afrika ta kasa reshen jihar Neja.
No comments