Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Hada Kai Da Kamfanonin Kasar Sin Don Habaka Tsaro, Noma, Sufuri Da Hakar Ma'adanai

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta no...

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma'adanai na jihar.

A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a ziyarar aiki a ƙasar Sin daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Fabrairun 2025, domin yin haɗin gwiwa a muhimman sassa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd yayin da suke ƙasar Sin.

Tang Zhangwei, ya jagoranci wasu kamfanoni zuwa jihar Zamfara, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a sassa masu muhimmanci, domin bunƙasa tattalin arziki.

A nasa jawabin, gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin da kamfanonin ƙasar Sin ke yi na tabbatar da nasarar haɗin gwiwarsu.

“Ina so in yi muku barka da zuwa Jihar Zamfara. Muna maraba da ku. A watan Fabrairu, na jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Sin don ganawa da kamfanoni a sassa daban-daban da kuma gano ci gaban da za su samar. Tafiya ce mai tasirin gaske.

“Mun yi haɗin gwiwa da kamfanin ƙasa da ƙasa na Zhong Zhao, wanda ya kware a fannin takin zamani da noman zamani. Suna mai da hankali kan samar da takin gargajiya da fasahar kiwo na R&D. Mun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin horar da manoman gida sana’o’in noma, ta hanyar amfani da injina da fasahar zamani wajen kafa masana’antar takin zamani a jihar Zamfara.

“Tawagar Zamfara ta yi hafin gwiwa da kamfanin Phoenix Wings, wani kamfanin ƙasar Sin da ya ƙware kan fasahar sa ido kan tsaro, gami da jirage marasa matuƙa. A tare, za su bullo da dabarun samar da ingantattu

No comments