Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gobe take Sallah a Nijeriya

An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da Æ™arewar watan azumi na Ramadanan bana. Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubak...



An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya aminta da ganin jinjirin watan Shawwal a yau Asabar 29 ga watan Ramadan 1446 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris 2025.

Sarkin Musulmi ya ce dangane da bayanan da suka samu na ganin wata a wurare daban-daban a Nijeriya daga Fadar Shehun Borno da Sarkin Zazzau da Ƙungiyar Izala mai hedikwata a Jos da sauran mutane don haka Azumin watan Ramadan ya zo ƙarshe daga yau Asabar.

Tun farko É—aya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ya sanar da hakan cikin wani saÆ™o da ya wallafa a shafinsa na X.

Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.

No comments