Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar ‘Yan Asalin Abuja Ta Caccaki Sojojin Nijeriya Kan Afkawa Masu Zanga-zanga, Sun Ce Abuja Ba Fagen Yaƙi Ba Ne

Ƙungiyar ‘yan asalin garin Abuja wato 'Concerned Abuja Indigenes' sun yi Allah wadai da mummunan lamarin hana zanga-zang...

Ƙungiyar ‘yan asalin garin Abuja wato 'Concerned Abuja Indigenes' sun yi Allah wadai da mummunan lamarin hana zanga-zangar lumana a babban birnin ƙasar, inda suka yi gargaɗin cewa bai kamata a mayar da Abuja filin yaƙi ba. Ƙungiyar ta caccaki yawan amfani da ƙarfin iko daga hukumomin tsaro kan masu zanga-zanga, kuma ta buƙaci adalci ga waɗanda aka afka wa a kwanan nan.

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar 3 ga Afrilu, 2025, wanda Ayedo Danjuma Abdul ya sanya hannu, ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta game da ayyukan rundunonin tsaro, musamman dangane da zanga-zangar da aka yi a ‘yan kwanakin nan, ciki har da zanga-zangar da aka fi sani da #EndBadGovernance, da ta masu tattakin Arba'een, da kuma zanga-zangar ranar Qudus ta Duniya.

“Abuja, babban birnin ƙasar mu mai albarka, an maishe shi fagen yaƙi, inda rundunonin tsaro ke yin ta’adi ga mutanen da ba su da laifi,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta zargi jami'an tsaro da kai hari haka siddan ga masu zanga-zangar neman sassaucin rayuwa. Haka kuma, ta zargi cewa a yayin tattakin arba'een wanda ‘yan Harkar Musulunci ke shiryawa waɗanda aka fi sani da ‘yan shi’a, rundunonin tsaro sun buɗe wuta kan masu tafiyar cikin lumana, inda suka kashe mutane biyu, suka jikkata da dama, sannan suka kama da dama ba tare da bin ƙa’idar doka ba.

“Waɗanda aka kama a lokacin tattakin arba'een suna cigaba da zama a kurkuku ba tare da bin ƙa’idar shari'a ba, wannan take haƙƙin su ne na ɗan Adam," in ji sanarwar.

Ƙungiyar ‘yan asalin Abuja har wala yau ta zargi rundunar 'Guards Brigade' da kai mummunan hari kan masu zanga-zangar ranar Qudus ta Duniya, inda ta ce an harbi masu zanga-zangar da motocin yaƙi.

“Rundunar 'Guards Brigade', wadda ke da alhakin kare manyan jami’an gwamnati na Nijeriya wacce ke amsar umurni daga shugaban ƙasa kawai, ta yi amfani da dukkanin nau’ikan makamai, ciki har da motoci masu ɗauke da makamai da aka tanada domin yaƙi, domin harbe masu zanga-zangar da ke ɗauke da alluna da kwallayen zanga-zanga kawai na nuna goyon baya ga al’ummar Gaza," in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta ce, wannan hari ya haifar da mutuwar mutane da dama, kama ɗaruruwan mutane, da kuma rauni mai tsanani, ciki har da wasu daga cikin mazauna Abuja da ba su cikin zanga-zangar.

“Sun kashe da dama, sun kama ɗaruruwan mutane, kuma sun bar wasu da raunuka masu tsanani. Waɗannan ayyukan na zalunci sun janyo asarar rayuka da dama daga cikin waɗanda ba su da laifi, ciki har da mazauna Abuja da ke gudanar da harkokin su na yau da kullum. Wannan ya isa haka nan!" in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fayyace wanda ya ba da umurnin wannan hari, musamman rawar da rundunar 'Guards Brigade' ta taka a yayin harbin masu zanga-zangar a ranar Qudus.

“Rundunar 'Guards Brigade' ta Sojojin Nijeriya tana amsa umurni ne kawai daga shugaban ƙasa, a don haka, muna buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana gaskiya kan wannan batu. Waye ya bayar da umurnin wannan kisan? Me yasa ake amfani da hukumomin tsaro domin daƙile zanga-zangar lumana?” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da sukar amfani da hukumomin tsaro wajen biyan buƙatun ƙasashen waje a maimakon fifita tsaro da haƙƙin ‘yan Nijeriya.

“A matsayin mu na ‘yan asalin Abuja wannan ba abin yarda bane. Ba za mu zuba ido muna kallon hukumomin tsaro na take haƙƙin ɗan Adam ba domin biyan buƙatun ƙasashen waje a maimakon buƙatun 'yan Nijeriya. Ba za mu bari waɗanda ba ‘yan asalin Abuja ba su mayar da garin filin yaƙi ba a maimaikon kare rayuwa da dukiyar al’ummar mu ba.”

Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Kula da Haƙƙin Ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi bincike da gaggawa dangane da hare-haren da jami’an tsaron suka aikata a kwanan nan, kuma sun buƙaci a hukunta waɗanda suka aikata laifin.

“Muna buƙatar adalci da bincike. Muna kira ga Majalisar Kula da Haƙƙin Ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike na musamman cikin gaggawa kan waɗannan hare-haren, a hukunta masu laifi, sannan a tabbatar da cewa irin wannan karya haƙƙin ɗan adam ba zai sake faruwa ba. Waɗanda suka aikata wannan kisan, raunatawa, da kame ba bisa ƙa'ida ba, dole ne su fuskanci cikakken hukunci."

Ƙungiyar ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da kare haƙƙin mazauna Abuja da kuma adawa da matakin soji a cikin garin. Sun kuma yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da al’ummar duniya da su ɗauki mataki kan abin da suka bayyana a matsayin zaluncin da gwamnati ke aikatawa.

“Ƙungiyar ‘yan asalin Abuja ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare haƙƙin al’umma ba. Za mu tsaya tsayin daka wajen adawa da ɗaukar matakin soji a garinmu da kuma zaluntar ‘yan ƙasar dake sauke haƙƙin su. Muna kira ga dukkan 'yan Nijeriya masu tunani mai kyau, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, da al'ummar duniya su fito fili su yi magana game da waɗannan ta'adi da kuma buƙatar a yi adalci.”

“Wannan take haƙƙin ya isa haka nan!” in ji sanarwar.

No comments