Daga Awwal Umar Kontagora Uwargidan gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris Ƙauran Gwandu ta jagoranci taron walimar bik...
Daga Awwal Umar Kontagora
Uwargidan gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris Ƙauran Gwandu ta jagoranci taron walimar bikin ɗaurin wasu ƴaƴa mata marayu guda hamsin da aka ɗaurawa aure a garin Ɗakingari da ke ƙaramar hukumar mulki ta Suru.
Uwargidan gwamnan ta bayar da gudunmawar naira miliyan biyar ga harkokin bikin marayun.
An gudanar da taron walimar ne a farfajiyar sakatariyar ƙaramar hukumar mulki ta Suru da ke garin Ɗakingari ranar juma'ar makon nan da ta gabata.
Da take jawabi a wurin walimar, uwargidan gwamnan tayi kira ga amaren da su kasance masu hakuri da juriya ga mazajensu tare da tabbatar tattaunawa akan duk wata matsala da za ta taso a yayin zamantakewar aurensu.
Ta kara da cewar ku zamo masu biyayya ga mazajen slku, fahimtar juna da kuma girmama juna a zamantakewar auren ku
Haka kuma ta kara da cewar ku zamo masu addini da kuma fahimtar irin nauyin da yake kan ku, ku kare mutuncin auren ku da kuma zama uwaye nagari ga ƴaƴan da zaku samu nan gaba.
Itama matar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Suru da Bagudo, Hajiya Aisha Bello Ka'oje da take a na ta jawabin, tayi kira ga amaren da su zamo masu biyayya, gaskiya da ɗa'a ga mazajensu.
Ta ƙara da cewar ku zamo masu taimakon mazajen ku, masu bayar da kyakkyawar tarbiyya ga ƴaƴan ku, da kuma kasancewa uwaye nagari ga ƴaƴan ku.
Hajiya Aisha Ka'oje ta Kuma yi kira ga matan su kasance masu gudanar da wasu sana'o'in hannu dan dogaro da kai a cikin gidajen su wanda hakan zai taimaka musu wajen magance wasu matsalolin su har ma su taimakawa mazajensu.
Daga karshe Hajiya Aisha Bello Ka'oje ta baiwa kowace amarya daga cikin amaren hamsin gudummawar naira dubu hamsin da zannunwan gado.
Matar shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Suru, tayi godiya ta musamman ga uwargidan gwamna bisa irin gudunmawar da take bayarwa ga al'ummar ƙaramar hukumar mulki ta Suru dama jihar Kebbi baki daya inda ta ƙara jaddada cigaba da bayar da goyon bayan ta ga gwamnatin Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu musamman manufofin gwamnatin na inganta rayuwar al'ummar jihar da kuma gudanar ayyukan cigaban al'umma.
Daga cikin ababen da aka gudanar a lokacin walimar sune zagayen duba kayan amaren da suka haɗa da kayan gadaje da kujeri da dai sauransu.
An gudanar da bikin ɗaurin auren ne ranar asabar a fadar sarkin Dakingari da ke karamar hukumar Suru.
No comments