Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Thursday, June 12

Pages

Labarai:

Ƙungiyar Jakadun Matasan APC Ta Taya Shugaban Jam'iyyar APC A Jihar Neja Murnar Samun Muƙami Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar matasa jakadun APC (APC Youth Ambassadors) ta ƙasa ta taya shugaban jam'iyyar APC a jihar Neja, Hon. Aminu Musa Bobi murnar karbar takardar kama aiki a matsayin shugaban gudanarwa na hukumar kula da dakunan ajiye littafai ta kasa ( National Library of Nigeria). Da yake bayyana jinjina ga shugaban kasa a madadin kungiyar, mataimaki na musamman ga shugaban kungiyar ta kasa, Comr. Muhammad Awwal Umar (Kontagora) yace wannan matsayin tukuici ne ga matasa da suka wahala wajen ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu nasara a babban zaben kasa da ya gabata.

Comr. Umar, ya cigaba da cewar tsarin siyasar Bola Ahmad Tinubu tsari ne na tafiya da kowa musamman wadanda suka bada lokacinsu wajen samun nasarar jam'iyyar APC.

APC Youth Ambassadors, ta shawarci shugaban kasa da ya cigaba da baiwa matasa dama musamman wadanda suka wahala da jajircewa wajen ganin APC ta samu nasara, dan karfafa guiwarsu da cire masu zargin wariya a wajen bada mukaman siyasa.

Comr. Umar Kontagora, yace jagoran tafiyar matasa jakadun APC na kasa, Injiniya Kabiru Abdulhamid ya hori matasa da su kara hakuri da cigaba da marawa jam'iyyar APC baya domin samun damar gina kasa da samar da shugabanci na gari musamman a shirin gwamnatin tarayya na karfafa guiwar yan Nijeriya (Hope Agenda) domin dawo da martabar kasar nan bisa tsarin mulkin dimukuradiyya.
Kungiyar APC Youth Ambassadors ta kasa ta hori gwamnatin jahohi da su yi koyi da irin salon tafiyar shugabanci irin na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu wajen ganin sun baiwa kungiyoyin matasa da suka wahala da jam'iyyar dan ganin ta samu nasara.

Comr. Umar Kontagora, ya ce shugaban kungiyar ta kasa ta jawo hankalin shugaban jam'iyyar APC na jihar Neja kuma Broad Chairman na hukumar National Library of Nigeria, da ya dauki salon tafiyar da shugabancin jam'iyyar APC a jihar Neja wajen cigaba da baiwa matasa damar samun mafaka, hakan zai kara ba shi damar samun kwarin guiwar gina yayan jam'iyyar da basu kwarin guiwar yin amanna da tsarin tafiyar jam'iyyar wajen ta tafi da kowa ta yadda za ta kara tasiri a zukatan al'umma da tabbatar da siyasa bisa adalci ba tare da nuna bambanci ba, tsakanin bowa da mora kamar yadda aka sabo a baya ba.
Kungiyar ta taya gwamnatin Neja, bisa jagorancin babban manomin jiha, Dakta Umar Mohammed Bago da jam'iyyar bisa samun wannan matsayin ga shugaban jam'iyyar ta jiha, Hon. Aminu Musa Bobi wanda ya kafa tarihi na hadin kan yayan jam'iyya da gwamnati wajen samar da gurabun mukaman siyasa ga yayan jam'iyya ta jiha.

No comments