Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Mai Suna Mati, Da Wasu Mayaƙa Da Dama, Sun Kuma Ƙwato Makamai a Zamfara. Dakarun soji ƙar...
Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Mai Suna Mati, Da Wasu Mayaƙa Da Dama, Sun Kuma Ƙwato Makamai a Zamfara.
Dakarun soji ƙarƙashin rundunar Operation Forest Yaki sun kaddamar da wani sabon samame mai suna “Operation Munzo” domin kawar da sansanonin ’yan ta’adda a jihar Zamfara.
An fara samamen daga Bagega a ƙaramar hukumar Anka, inda dakarun suka kutsa zuwa kauyukan Tibuki da Sabuwar Tunga, har zuwa sansanin sanannen ɗan ta’addan mai suna Mati.
An samu gagarumar nasara wurin fafatawar, inda dakarun soji suka fi ƙarfin ‘yan ta’addan, inda suka kashe da dama daga cikinsu, ciki har da Mati, wanda ake zargi da kai hare-hare da dama a yankin.
Wani soja daga Special Boat Service ya samu rauni a ƙasa da ƙirji, amma an kai shi asibiti kuma yana samun sauƙi.
Sojoji sun kwato bindigar PKT guda ɗaya da albel guda biyu, bindigogi AK-47 guda biyar, majinyoyi 12 da harsasai 487, na’urorin sadarwa Baofeng guda uku, da khaki na soja da ’yan sanda. Sun kuma ƙone babura uku, sun samo wasu shanu da aka sace.
An lalata duk wata cibiyar sadarwa da ‘yan ta’adda ke da ita a sansanin Mati. Sai dai wasu motocin dakarun sun samu ɗan lalacewa.
A wani hari dabam da aka kai wa motocin sojin dake ɗauke da kayan aiki daga Bagega zuwa Dan Gulbi anyi musu kwanton bauna a kusa da wata gada, amma dakarun sun yi nasarar fatattakar maharan. Soja ɗaya ne ya ji rauni kuma yana cikin koshin lafiya.
“Operation Munzo” na ci gaba da gudana domin murkushe sansanonin ‘yan ta’adda a dazukan Zamfara.
No comments