Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Waɗanda Suka Yi Muzaharar Goyon Bayan Falasɗinu Na Mutuwa A Hannun 'Yan Sandan Abuja, In Ji Harkar Musulunci

Harkar Musulunci ta bayyana damuwa game da rahoton mutuwar wasu daga cikin masu muzaharar goyon bayan Falasɗinu da ke tsare a ha...

Harkar Musulunci ta bayyana damuwa game da rahoton mutuwar wasu daga cikin masu muzaharar goyon bayan Falasɗinu da ke tsare a hannun rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya (FCT).

A cewar wata sanarwa da Shaikh Sidi Munir Mainasara ya rattaba hannu a madadin Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky, a ranar Talata 8 ga Afrilu, 2025, aƙalla mutum guda daga cikin masu muzaharar da aka kama ya mutu a hannun 'yan sanda tun bayan kamun da aka yi a ranar 28 ga watan Maris, 2025.

“Mun samu labari mai matukar girgiza cewa masu muzaharar goyon bayan Falasɗinu da aka kama tun daga ranar 28 ga Maris, 2025 wadanda ke hannun rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya suna mutuwa a yayin da ake tsare da su,” in ji sanarwar.

“Daga cikin wadanda suka rasa ransu a kwanan nan akwai Shaheed Huzaifa Muhammad daga Tudun Iya, jihar Katsina, wanda ya rasa ransa a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 6 na yamma a SARS Abattoir, Guzape, Abuja.”

Harkar Musulunci ta tunatar da cewa a ranar Juma’a, 28 ga Maris, dakarun Guards Brigade na sojojin Nijeriya suka kai hari ba tare da wani dalili ba kan taron ranar Kudus ta duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a masallacin Usman Bin Affan da ke kan titin Aminu Kano Crescent a Abuja.

“A yayin harin, sojoji sun kashe masu muzaharar 26 tare da kama 274, ciki har da ƙananan yara 60; wanda ya haɗa da marasa lafiya 11 da har yanzu suke tsare duk da mummunar rashin lafiyar da suke fama da ita,” in ji sanarwar. “Har yanzu dai, sojoji da ‘yan sanda sun ki sakin masu muzaharar da aka kama da kuma gawarwakin wadanda suka kashe.”

Sanarwar ta jaddada cewa “laifin” kawai wadanda aka kashe ko aka tsare shi ne halartar muzaharar ranar kudus ta duniya tare da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu.

“Ayatollah Khomeini ne ya assasa ranar kudus ta duniya a shekarar 1979. Kuma ranar kudus ta duniya rana ce ta nuna goyon bayan al’ummar duniya ga al’ummar Falasɗinu, kuma ana gudanar da ita cikin lumana a kasashe fiye da 80,” sanarwar ta bayyana.

“Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Maulana Sayyid Ibraheem Zakzaky ta dade tana gudanar da wannan muzaharar fiye da shekaru arba’in. A bana ma, an gudanar da muzaharar Kudus a jihohi fiye da 17 a Nijeriya, ciki har da manyan birane irin su Legas, Kano da Sakkwato, ba tare da wani rikici ba.”

Sanarwar ta kuma ambato kalaman Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tugar, wanda ya shaida wa Al Jazeera a birnin Doha, a Qatar, cewa “Isra’ila dole ne ta dakatar da yaki da take yi a Gaza, kuma duniya ta daina nuna wariya dangane da kisan da ake yi a yankin da aka mamaye.”

“To amma abin mamaki,” in ji Harkar Musulunci, “a watan Maris 2025, Nuhu Ribadu, mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan tsaro, ya umurci jami’an tsaro da su kai hari kan masu muzaharar goyon bayan Falasɗinu a Abuja.”

A ƙarshe, Harkar Musulunci ta ce shugaban kasa shi ne yake da alhakin kashe rayukan da aka rasa, kuma ta jaddada cewa za ta ɗauki matakin doka da kuma gudanar da addu’o’i kan kisan da aka yi:

“Za mu ɗora alhakin kisan da aka yi a kan Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ke da alhakin kisan masu muzaharar nuna goyon bayan Falasɗinu guda 27, kuma za mu yi addu’ar la’ana akan duk wanda ya bayar da umurni ko ya aiwatar da kisan da kuma kama mahalarta muzaharar ranar Kudus ta duniya na 2025 da aka yi a Abuja.”

“A yayin da muke la’antar wannan mugun aiki da ya saba wa ‘yan adamtaka, muna kuma shirin gurfanar da duk masu hannu a cin zarafin dan Adam da aka yi wa masu muzaharar a gaban kotu,” sanarwar ta tabbatar.

No comments