Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga shugaban kasa da ya ji tsoron Allah akan tsare tsaren mulkinsa, ba wani cigaban da aka samu ko sauki...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga shugaban kasa da ya ji tsoron Allah akan tsare tsaren mulkinsa, ba wani cigaban da aka samu ko saukin rayuwa ga talaka, domin komai ya tsaya cak a kasar nan. Dr. Umar Farooq Abdullahi yayi kiran a lokacin rufe tafsirin Alkur'ani karo na ashirin da bakwai da harshen Nupanchi.
Malamin, ya cigaba da cewar abin takaici wanda idan shugaban kasa ya manta dole a tunatar da shi, al'ummar musulmi sun tsaya kai da fata wajen ganin kafuwar mukinsa kan haka aka kira gwamnatin da Muslim Muslim Ticket, amma yau saboda giyar mulki ba mai dandana kudarsa a hannun gwamnatin Tinubu kamar al'ummar musulmi.
Kasar da ba tsaro, ba rayuwa mai inganci, ba ruwan sha kuma wadataccen wutan lantarki, wani cigaba aka samu alhalin a kullun rayuwa kara tsada take ga talaka wani riba aka samu da za a nunuwa duniya cewar Nijeriya ta samu, maganar gaskiya da dole mu fada tsarin tafiyar da mulkin nan akwai gyara, a dawo mana da tallafin man fetur, a dawo mana da tallafin kujerar Hajji, dole ayi abinda ya dace da yan Nijeriya zasu samu walwala, aminci da yan uwantaka na kasa ya dawo jikin yan Nijeriya.
Amma idan an ki lallai wannan tafiyar ba za ta haifar da da mai ido ba, domin talaka va zai yafe ba muddin ba a tausaya masa akan irin ukubar da yake ciki ba, inji shi.
Abin bakin ciki da takaici, kasa kamar Ghana wanda John Mahma ke mulki, wanda ba musulmi ba ne alkawali yayi idan ya samu nasarar zabe, zai rage kudin aikin Hajji, kuma yayi kowa ya shaida, amma a Nijeriya sabanin hakan, kasar da Musulmi ne shugaban kasa da mataimakinsa a ce aikin Hajji na son gagarar musulmi, gaskiya akwai bukatar shugaban kasar Nijeriya ya dawo cikin hayacin shi.
Tunda daga cire tallafin man fetur tsare tsaren gwamnati ya sake hanya, abubuwan suja damalmale domin talakan Nijeriya ba abinda yake dandanawa da wannan tsarin face ukuba.
Malamin, ya cigaba da cewar yan majalisar dokokin kasa ba aikin da su ke yi na daidaita kasa. Wallahi yan majalisar dattijai da na wakilai su ji tsoron Allah, wannan hanyar da suke akai talaka ya zabe su ba.
Kasar nan muna bukatar jajirtattun yan majalisa masu kishin kasar da gaskiya ba yan amshin shata ba.
Umar Farooq Abdullahi Nupe Tafsir Organisation ta yabawa gwamnatin jihar Neja bisa jajircewa da aiki tukuru wajen an samar da sabuwar jihar Neja, dan haka babban manomin jiha, Dr. Umaru Mohammed Bago na bukatar goyon baya da addu'o'in samun nasara.
Taken tafsirin na bana dai shi ne yiwa kasa addu'o'i, dan samun zaman lafiya, hadin kai da cigaban jihar Neja da kasar nan baki daya.
Shi dai tafsirin da ake gabatarwa da harshen Nupe ya kwashe shekaru ashirin da bakwai da farawa.
Da yake karin haske, Sheikh Abu Sumayya, yace idan ma mutum yana ganin Muslim Muslim Ticket bai yi tasiri ba, malaman addini zasu jira akwai lokacin da za a nemi gudunmawarsu.
Amma maganar gaskiya manufar da aka zabi gwamnatin nan ya saba ma wanda ake gani a yanzu, don haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bude idonta daga hanyar da tunkara, ba zai yi yiwu mun zabi gwamnati dan ganin sauyi da cigaban kasa amma ya zama ta kama hanyar kurkusar da al'umma mu yi shiru ba.
Da ya juya kan tsare tsaren gwamnatin Neja kuwa, yace gwamna Umaru Bago baya bukatar sharhi face sambarka da cigaba da goya masa baya, da addu'o'in samun nasarar ayyukan da sanya a gaba.
No comments