Daga Zainab Rauf, Abuja Dandalin Resource Forum na Harkar Musulunci ta yi Allah wadai da harin da rundunar sojojin Nijeriya (Guard Brigade...
Daga Zainab Rauf, Abuja
Dandalin
Resource Forum na Harkar Musulunci ta yi Allah wadai da harin da rundunar sojojin
Nijeriya (Guard Brigade) ta kai kan masu muzaharar ranar Kudus ta duniya ta
2025 a birnin Tarayya Abuja. Harin, wanda ya auku a ranar Juma’a, 28 ga watan Maris,
ya haifar da asarar rayuka da kuma raunuka da kuma kama daruruwan masu muzaharar.
Harkar
Musulunci ta yi wannan Allah wadai din ne a yayin wani taron manema labarai da
ta gudanar a Abuja a yau Asabar. A cikin wata sanarwa da Farfesa Abdullahi
Danladi ya sanyawa hannu, Harkar musulunci ta bayyana cewa: “Muna yin Allah
wadai da harin da Guard Brigade ta kai kan masu muzaharar ranar Kudus ta duniya
ta 2025 a Abuja.”
A
cewar sanarwar, “a jiya, 28 ga Maris 2025, wanda ya kasance Juma’ar karshe na
watan Ramadan 1446H, ya kasance ranar Kudus ta duniya, rana da Imam Khomeini
(QS) ya ware domin nuna goyon baya ga wadanda ake zalunta a duniya, musamman
Falasdinawa. Ana gudanar da muzaharar ranar Kudus a kasashe daban-daban kamar
Biritaniya, Faransa, Amurka, Jamus, Ostiraliya, Sweden, Kanada da kuma kasashe
da dama a Asiya, Afirka, Latin Amurka da Gabas Ta Tsakiya.”
“Harkar
Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky tana gudanar da muzaharar
ranar Kudus ta duniya sama da shekaru 40 a Nijeriya. Sai dai a bana, an gudanar
da muzaharar cikin lumana a duk fadin Nijeriya, sai dai Abuja kadai aka afka
mata.”
Sanarwar
ta bayyana yadda muzaharar ta fara: “An fara muzaharar ranar Kudus ta duniya ta
2025 a Abuja cikin kwanciyar hankali daga Masallacin Usman Bin Affan da ke kan
titin Aminu Kano Crescent, Wuse 2, Abuja. Bayan ƴan mintuna da fara muzaharar,
sai wasu dakarun Sojojin Nijeriya (Guard Brigade) suka kawo hari, suka yi
amfani da harsasai masu rai. Mutane da dama sun ji munanan raunuka daga harbin
bindiga, wasu kuma sun rasa rayukansu sakamakon wannan zalunci. Baya ga kashe
masu muzahara da ba su da makamai, sojojin sun kuma aikata munanan abubuwa
kamar cafke mata a cikin harabar masallacin Usman Bin Affan, dukan mata da
yara, cire hijabi daga jikinsu a wajen masallacin; wadannan ayyukan laifi ne a
addinin Musulunci da dabi’un Musulmi.”
Sanarwar
ta karyata rahotannin da ke cewa an yi artabu: “Ba kamar yadda wasu kafafen yada
labarai suka ruwaito ba cewa an yi artabu, babu wani abu da masu muzahara suka
aikata da zai haifar da wannan zalunci. Hakika, masu muzaharar Kudus, wadanda
suka hada da maza, mata da yara, Musulmi da Kiristoci, suna tafiya cikin lumana
daga masallacin bayan sallatar Jumu’a inda suka nufi kasuwar Wuse, kwatsam sai
sojojin suka tare su da wata motar yaki sannan suka fara bude wuta kan masu
muzaharar, da dama daga cikinsu mata da yara ne.”
Sanarwar
ta kara da cewa: “A ranar 27 ga Maris 2025, wata wasika daga ofishin mai ba da
shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA) da ta bayyana a shafukan sada zumunta,
tana umartar jami’an tsaro da su dauki matakin da ya dace kan muzaharar Kudus
Ta Duniya da za a gudanar. Wasikar mai lamba NSA/366/S, wadda aka aikawa dukkan
hukumomin tsaro, ta bayyana cewa ‘akwai bayani cewa Harkar Musulunci ta shirya
gudanar da muzahara a ranar Juma’a, 28 ga Maris, 2025 a jihar Nasarawa da Abuja
don nuna goyon baya ga Falasdinu.’ Wasikar ta kara da cewa ‘An bukaci a dauki
matakin da ya dace kan lamarin.’”
Harkar
Musulunci ta bayyana cewa an shirya wannan hari tun farko dama: “Tun bayan
bayyanar wannan wasika, jami’an tsaro, musamman a Abuja, sun shirya don aikata
wadannan laifuka a harabar Masallacin Usman Bin Affan. Wannan za a iya gani
daga yadda aka jibge jami’an tsaro a Masallacin Kasa na Abuja da wasu
masallatai a cikin birnin.”
Harkar
Musulunci ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana da munafunci a manufofinta na hulda
kasashen waje: “Abin mamaki ne yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke nuna sabani
a manufofinta. A yayin da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tugar,
ke cewa a cikin wata hira da Al-Jazeera a birnin Doha, a Qatar a watan Maris
2025 cewa ‘Isra’ila dole ta dakatar da yakin da take yi a Gaza, kuma duniya ta
daina nuna son kai kan kisan gillar da ake yi a yankin,’ sai kuma NSA ke bayar
da umarnin kai hari kan masu muzaharar ‘Free Palestine’ a Abuja.”
Game
da adadin mutanen da aka kashe da wadanda aka kama kuwa, sanarwar ta bayyana
cewa: “Bayanan da aka tabbatar sun nuna cewa Guard Brigade da ƴan sanda sun
cafke mutane 380, ciki har da mata da yara, a yayin da mutane hudu aka tabbatar
sun rasa rayukansu. Wadanda aka kama suna tsare a SARS Abbator, Guzape, Abuja.
Wadanda aka kashe kuwa sun hada da Shaheed Ibraheem Dalhat (Sharif Albani),
Shaheed Nasir Abubakar, Shaheed Abdulaziz Abubakar, da Shaheed Auwal Abbas
Bichi. Duk da haka, jami’an tsaro na boye wasu gawarwakin da yawa na mutanen da
suka kashe wanda bai gama bayyana ba. Za mu ci gaba da sanar da al’umma kan
sabbin bayanai da suka shigo.”
Harkar
musulunci ta dora alhakin wannan hari kan shugaban kasa: “Muna dora alhakin
wannan kisan kai da cin zarafi ga addinin Musulunci da dabi’un musulmi ga Bola
Ahmed Tinubu, wanda ya ba da dama ga Guard Brigade su aikata wadannan ta’asa
yayin harin da suka kai a Masallacin Usman Bin Affan, Abuja.”
Sanarwar
ta karkare da cewa: “A bisa haka, muna bukatar a saki duk wadanda aka kama ba
tare da wani sharadi ba dangane da muzaharar Ranar Kudus Ta Duniya da aka
gudanar a Abuja a ranar 28 ga Maris, 2025. Haka kuma, muna bukatar a hukunta
duk masu hannu a kashe-kashen da aka yi wa masu muzaharar ‘Free Palestine’.”
No comments