Daga Zaharaddeen Sirajo Abbas Ƙungiyar Matasa ta ƙasa (NYCN) ta yi gargaɗi kan wasu ayyukan damfara da wasu ‘yan damfara ke yi...
Daga Zaharaddeen Sirajo Abbas
Ƙungiyar Matasa ta ƙasa (NYCN) ta yi gargaɗi kan wasu ayyukan damfara da wasu ‘yan damfara ke yi a matsayin shugabannin reshen jihar Katsina na ƙungiyar.
Sanarwar da NYCN ta fitar daga hedikwatar ta ƙasa, wacce Shugaban NYCN na ƙasa Amb. Sukubo Sara-Igbe Sukubo da Sakatare Barista Suleiman Abubakar suka rattaba hannu, ta bayyana cewa waɗannan ‘yan damfara suna shirya wani zaɓen bogi domin naɗa sabbin shugabanni a reshen Katsina.
NYCN ta bayyana cewa babu wani zaɓe da aka shirya a yanzu a Katsina, kuma ƙungiyar NYCN ta ƙasa ce kawai ke da ikon shiryawa da kuma sanar da irin waɗannan zaɓuka.
Ƙungiyar ta ce ta riga ta sanar da Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Dikko Umar Radda, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, da Daraktan Hukumar DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Katsina.
NYCN ta gargaɗi dukkan matasa da ƙungiyoyin matasa a Katsina da su guji shiga duk wani taro da waɗannan ‘yan damfara suka shirya.
A ƙarshe, NYCN ta buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare zaman lafiya da amincin matasan jihar Katsina. Ta kuma buƙaci matasa su zama masu lura da bayar da rahoton duk wani mutum ko abu da ke da alaƙa da wannan damfara.
Har wala yau sanarwar ta tabbatar da cewa Kwamared Shamsu Ibrahim Shamo shi ne sahihi kuma zaɓaɓɓen shugaban NYCN reshen jihar Katsina. "Babu wani zaɓe da aka shirya ko ake gudanarwa a halin yanzu," in ji majalisar, tare da ƙarin bayani cewa hedikwatar ta ƙasa ta NYCN ita ce kaɗai ke da ikon tsarin mulki na kula da duk wani zaɓe da za a gudanar a nan gaba a reshen jihar.
No comments