Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi Za Ta Mayar Da Al'ummar Da Harin Ƴan Ta'addan Lakurawa Ya Raba Da Garuruwan Su

Daga Awwal Umar Kontagora   Gwamnan Kebbi, Kwamared Nasir Idris Ƙauran Gwandu  ya bayyana gwamnatin sa a shirye take wajen mayar...

Daga Awwal Umar Kontagora 

Gwamnan Kebbi, Kwamared Nasir Idris Ƙauran Gwandu  ya bayyana gwamnatin sa a shirye take wajen mayar al'ummomin hare haren yan ta'addan Lakurawa ya raba da muhallansu, gwamnan ya bayyana hakan ne ranar laraba makon nan lokacin da ya kai ziyarar jaje a sansanin ƴan gudun hijira dake cikin garin Kangiwa inda al'ummar garuruwan Birnin Debe, Ɗan marke da Tambo suke gudun hijira.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar jajen, Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya bayyana cewar gwamnatin Kebbi tana cigaba da shirye-shiryen sake tsugunar da al'ummar da ke gudun hijirar sanadiyyar hare-haren ƴan ta'addan Lakurawa zuwa kauyukan su.

Yan ta'addan na Lakurawa sun kai harin ne garuruwan Birnin Debe, Ɗan marke da Tambo da ke ƙaramar hukumar mulki ta Arewa ranar asabar da ta gabata inda suka kashe aƙalla mutane goma sha daya tare da kuma ƙone daya daga cikin garuruwan.

Gwamnan ya bayyana cewar babban dalilin kawo ziyarar tashi itace domin yiwa al'ummar jaje da kuma ta'aziyar rashin mutanen da suka yi tare kuma da ganewa idon sa halin da al'ummar suke ciki domin ɗaukar matakan da suka dace.

Gwamnan ya nuna takaicin sa bisa irin yadda ƴan ta'addan suke hallaka rayuka da dukiyoyin al'umma a duk lokutan da suka kai hare-haren inda kuma ya yabawa jami'an tsaro bisa irin kokarin da suke yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Gwamnan ya ƙara da cewar Yan ta'addan suna shigowa ne daga makwabtan jihohi irin Sakkwato da kuma Jamhuriyar Nijar.

Gwamnan ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Arewa bisa samar da sansanin ƴan gudun hijira a Kangiwa kamar yadda aka ba shi umurni.

Haka kuma nan take gwamnan ya bayar da umarnin a sawo karin kayan abinci da suka haɗa da buhun shinkafa da gero dari  da kuma shanu domin yankawa al'ummar ƴan gudun hijira. 

Haka kuma yace za'a dinga yin haka a kowane kwanaki huɗu zuwa biyar a sansanin gudun hijirar.

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatin jihar za ta yi duk ƙoƙarin da ya dace wajen ganin al'ummar ƴan gudun hijira sun koma garuruwansu nan da sati biyu.

Haka kuma yayi kira ga al'umma da su dinga baiwa jami'an tsaro bayanan dukkanin wani abu da ba su aminta da shi domin ɗaukar matakan da suka dace.

Ƙauran Gwandu ya bayyana cewar gwamnatin jihar Kebbi za ta taimakawa al'ummar da aka ƙone garin na su wajen sake gina gidajen nasu domin cigaba da gudanar da rayuwar su a inda suka saba.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin sawo kayan goyo da kuma raguna biyu fa dukkanin maccen da haihuwa ya kamata a sansanin gudun hijirar domin bikin sunan yaran.

Tun a farko, da yake nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Arewa, Alhaji Sani Aliyu, ya yabawa gwamna  Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa matakan gaggawa da ya ɗauka wajen magance wannan matsalar tsaro.

Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara jinjinawa gwamna bisa ziyarar jaje da ta'aziya da ya kai a wasu kauyukan da aka kai harin kwanakin baya a ƙaramar hukumar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane shida.

Yayi godiya ga gwamna bisa umarnin da ya ba shi na samar da sansanin gudun hijira wanda sakataren gwamnatin Kebbi ya kula da samar da dukkanin abinda ya dace a wurin.

Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana yadda za'a raba kuɗin tallafin da aka samu. Wanda yace za a raba tallafin GA Iyalan da suka rasa wani daga cikin ƴan uwansu a wannan harin, za'a ba su gudunmawar Naira dubu ɗari biyar.
Waɗanda suka samu raunuka daban-daban a sanadiyar harin za'a basu gudunmawar Naira dubu ɗari biyar ko wannensu.
Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewar sakataren gwamnatin Kebbi ya samar da buhun shinkafa guda hamsin wanda za'a din ga amfani da shi wajen ciyar da al'ummar ƴan gudun hijira.

Wasu daga cikin ƴan gudun hijirar da suka haɗa da Aliyu Sani Birnin Debe, Buhari Muhammad da Halima Musa sun bayyana yadda ƴan ta'addan suka kawo hari ƙauyukan tare da sanyawa gidajen mutane wuta wanda haka ya haddasa mummunan tashin hankali ga al'ummar garuruwan.

Daga karshe sun yi godiya ta musamman ga gwamna bisa ziyarar jaje da ta'aziya da ya kawo musu da kuma tallafin da aka samar musu inda suka yi kira da a kara samar musu da taimako da kuma matakan tsaro.

No comments