Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yaba Wa Gwamna Umaru Bago Bisa Ƙoƙarin Tabbatar Da Haɗin Kan Ƴaƴan Jam'iyyar APC A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora   An yabawa gwamna Umaru Mohammed Bago bisa kokarin ganin hadin kan yayan jam'iyyar APC a jihar Ne...

Daga Awwal Umar Kontagora 

An yabawa gwamna Umaru Mohammed Bago bisa kokarin ganin hadin kan yayan jam'iyyar APC a jihar Neja, duba da irin matakan da yake dauka na ganin zaben shugabannin kananan hukumomi da kansuloli bai zamo sanadin rarrabuwan kawunan yayan jam'iyya ba. 

Daya daga cikin yan takarar shugabancin karamar hukumar Lavun, Hon. Zakari Mohammed Kuchi ne yayi yabon lokacin da yake zantawa da manema labarai ra'ayinsa dan gane da shirye shiryen zaben shugabannin kananan hukumomi mai zuwa,  bayan wani zaman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a karamar hukumar Lavun. 

Yace duk da cewar gwamna ya baiwa jam'iyyar ta APC shawarar ayi consensor,  wanda hakan yana da kyau, kuma ina da kwarin guiwar wadanda jam'iyya ta damkawa alhakin kula da wannan sulhun, zasu ba ni damar samun tikitin takara tunda jam'iyya tace ba karba karba a matakin kananan hukumomi da gundumomi. 

Saboda haka, ina jawo hankalin al'ummar Kutigi da Doko da mu hada kai musamman dan ganin jam'iyyar mu ta APC ta samu nasara a wannan babban zaben mai zuwa. 

Ina tabbatarwa jam'iyyar APC a matakin jiha, bisa jagorancin Hon. Aminu Musa Bobi, da jagorancin karamar hukumar Lavun idan na samu tikitin takara kuma har na kai ga cin zabe,  zan tabbatar na dauki salon jagoranci irin na babban manomin jiha, Dakta Umaru Mohammed Bago, wajen farfado da martabar noma,  samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnatin, da tabbatar da ganin mun cigaba da kafa harsashen samar da sabuwar jihar Neja, dan inganta rayuwar al'umma da bunkasar tattalin arzikin kasa.

No comments